Kamfen: Mai dakin Ganduje ta yiwa matan Kano wani babban albishir

Kamfen: Mai dakin Ganduje ta yiwa matan Kano wani babban albishir

Uwargidan gwamnan Jihar Kano, Hafsat Ganduje tayi yiwa matan jihar alkawarin cewa za ta tabbatar anyi musu karin nadin mukamai idan mijinta ya yi nasarar lashe zaben shekarar 2019.

Mrs Ganduje tayi wannan alkawarin ne yayin da ta ke jawabi a wurin wani shirin tallafi ga mata 1,500 da akayi a karamar hukumar Dawakin Tofa na jihar a ranar Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa dan majalisar wakilai mai wakiltar Tofa/Dawakin Tofa/Rimin Gado, Tijjani Abdulkadir-Jobe ya tallafawa mata 1,500 da N10,000 kowanensu.

Mai dakin Ganduje ta yiwa matan Kano wani albishir

Mai dakin Ganduje ta yiwa matan Kano wani albishir
Source: Twitter

Ta ce, "Idan Gwamna Abudllahi Ganduje ya lashe zabe, zamu tabbatar cewa an kara bawa mata mukamai a cikin gwamnati."

DUBA WANNAN: Arzikin Dangote ya yi kasa, na Adenuga ya yi sama - Kiyasin Forbes

Ta ce bawa mata mukamai zai basu damar bayar da irin tasu gudunmawar wurin cigabar jihar da kasa baki daya.

"Ina son amfani da wannan damar in baku shawara ku zabi Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Abdullahi Ganduje domin hakan zai basu ikon cigaba da lasa muku romon demokradiyya musamman bangaren ayyukan more rayuwa," inji ta.

Ta ce a shekarar 2015, matsaloli da yawa sun kunno kai a kasar amma addu'ar mutane ya ceto Najeriya daga fadawa cikin fitina.

"Allah cikin ikon sa ya bamu Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa da Abudllahi ganduje a matsayin Gwamnan jihar Kano.

"Saboda haka sai mu cigaba da addu'io'in ganin cewa sunyi nasara a babban zaben shekarar 2019 domin su cigaba da ayyukan da suka fara," a cewar uwar gidan gwamnan.

Tayi kira ga dukkan mata da yara da shekarunsu ya isa kada kuri'a su fito kwansu da kwarkwata su zabi 'yan takarar jam'iyyar APC a babban zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel