An dora alhakin tsiyatar da Dangote kan Buhari

An dora alhakin tsiyatar da Dangote kan Buhari

Da dama masu sharhi kan al'amurran da suka shafi al'umma a shafukan sada zumunta musamman Twitter suna dora laifin raguwar kudin Aliko Dangote a kan salon mulkin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Tun farko dai mun kawo maku labarin cewa amshakin dan kasuwar nan a Najeriya Aliko Dangote har yanzu shi ne wanda ya fi kowa kudi a Afirika amma yawan kudin nasa sun ragu.

An dora alhakin tsiyatar da Atiku kan Buhari

An dora alhakin tsiyatar da Atiku kan Buhari
Source: Getty Images

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun yi magana game da harin su Shekau a Maiduguri

Legit.ng Hausa ta samu cewa Mujallar Forbes ta wannan shekarar ta wallafa cewa har yanzu sunan Dangote ne a farko a jerin masu kudin Afirika da dala biliyan 10.3.

Wannan na nuna cewa kudin nasa sun ragu da kusan dala biliyan 2.

Mujallar Forbes din ta nuna cewa matsalar kasuwa ce da kamfanin siminti na Dangote ya fuskanta ya jawo raguwar kudin.

Mike Adenuga, shugaban kamfanin sadarwa na Globacom shi ne yazo na biyu a jerin sunayen masu kudin da kusan dala biliyan 9.2.

A bara dai jimlar kudin Mike din dala biliyan 5.3 ne.

Ga dai ra'ayin wasu nan a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel