An yi harbe-harbe yayin da wasu matasa suka yi yunkurin rushe ofishin kamfen din Atiku

An yi harbe-harbe yayin da wasu matasa suka yi yunkurin rushe ofishin kamfen din Atiku

Jam'iyyar PDP ta koka a kan wani farmaki da wasu matasa suka kai ofishins yakin neman zaben Atiku dake Akure, babban birnin jihar Ondo.

Kakakin yakin neman zaben Atiku a jihar, Kayode Fasua, ya bayyana cewar wasu 'yan bangar siyasa dauke da makamai da suke zargin na yiwa jam'iyyar APC aiki ne suka kai farmakin da tsakar dare.

"Sun kawo harin da tsakar dare a lokacin da masu gadin mu sun tashi daga aiki. Sun kai kimanin su 10, kuma suna dauke da makamai, sun far wa wani maigadi da ya rage, sun yi masa duka sun daure shi.

An yi harbe-harbe yayin da wasu matasa suka yi yunkurin rushe ofishin kamfen din Atiku

An yi harbe-harbe yayin da wasu matasa suka yi yunkurin rushe ofishin kamfen din Atiku
Source: Facebook

"Bayan haka, sun lalata allunan tallar Atiku sannan sun yaga fastocinsa. Hakan bai ishe su ba saida suka lalata ginin ofishin domin neman wasu takardu, amma bayan burinsu bai cika bane sai suka fara harbin iska kafin daga bisani su gudu," a cewar Fasua

An yi harbe-harbe yayin da wasu matasa suka yi yunkurin rushe ofishin kamfen din Atiku

An yi harbe-harbe yayin da wasu matasa suka yi yunkurin rushe ofishin kamfen din Atiku
Source: Facebook

An yi harbe-harbe yayin da wasu matasa suka yi yunkurin rushe ofishin kamfen din Atiku

An yi harbe-harbe yayin da wasu matasa suka yi yunkurin rushe ofishin kamfen din Atiku
Source: Facebook

Fasua ya roki jami'an tsaro da su gudanar da bincike domin gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

Sai dai, a nata bangaren, jam'iyyar APC ta karyata cewar magoya bayanta suka aikata hakan ga ofishin kamfen din Atiku.

DUBA WANNAN: Mutane 10 sun mutu a wurin taron gangami na APC a Katsina

Sakataren yada labaran jam'iyyar APC a jihar Ondo, Alex Kalejaye, ya yi watsi da harin, amma ya ce babu hannun jam'iyyar APC a cikin kai harin.

"Bamu da hannu a cikin harin da aka kai ofishin kamfen na Atiku. Mun yiwa jama'a aiki, a saboda haka bamu da wata fargaba dangane da zabe mai zuwa," a cewar Kalejaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel