Dalilin da yasa gwamnonin APC basu halarci taron kamfen din Buhari ba - Oshiomhole

Dalilin da yasa gwamnonin APC basu halarci taron kamfen din Buhari ba - Oshiomhole

- Shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, yace gwamnonin APC sun kaurace ma taron kungiyar kamfen din shugaban kasa ne saboda su gwamnoni ne

- Ba a ga gwamnan APC ko daya ba yayinda Buhari ya jagoranci taron kungiyar kamfen dinsa

- Oshiomhole yace gwamnonin na jagorantar kamfen a jihohinsu daban-daban

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, yace gwamnonin APC sun kaurace ma taron kungiyar kamfen din shugaban kasa ne saboda su gwamnoni ne.

Babu gwamnan APC ko daya da ya halarci taron kungiyar kamfen din shugaban kasa da aka gudanar a yau Alhamis, 10 ga watan Janairu wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari da kansa ne yayi jagoranci.

Dalilin da yasa gwamnonin APC basu halarci taron kamfen din Buhari ba - Oshiomhole

Dalilin da yasa gwamnonin APC basu halarci taron kamfen din Buhari ba - Oshiomhole
Source: Facebook

Da aka tambayi dalilin da yasa gwamnonin suka ke zuwa, Mista Oshiomhole yace, “Saboda su gwamnoni ne, suna shugabantar jihohinsu.

“Kada ku manta ba a Abuja ake zabe kawai ba, zai gudana ne a jihohi 36 sannan ina da tabbacin akwai mambobin APC wadanda ke kamfen din majalisun dokokin kasa na da gwamna.

KU KARANTA KUMA: Kada ku zabi barayin shugabanni, ku zabi Buhari – Adamu

“Don haka kawo su Abuja ba zai taimaka ba. Anan, game da manufofi ne za a isar dasu ga fadin jihohi 6 da ke kasa, da kuma kananan hukumomi 774,” inji shi.

Mista Oshiomhole yace taron ranar Alhamis anyi shi ne domin tattauna ayyuka da kalandar kamfen a fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel