Zaben 2019: Muna da tabbacin nasara – Buhari

Zaben 2019: Muna da tabbacin nasara – Buhari

- Shugaba Buhari ya bayyana cewa yana da tabbacin yin nasara a zaben shugaban kasa na ranar 16 ga watan Fabrairu

- Ya yi magana a Abuja a wajen kaddamar da kungiyar kamfen din sa

- Sai dai kuma gwamnonin jam’iyyar APC ba su halarci taron ba, koda dai Oshiomhole yayi bayanin cewa aikin kamfen ya sha kan gwamnonin a jihohinsu daban-daban

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana da tabbacin yin nasara a zaben shugaban kasa na ranar 16 ga watan Fabrairu.

Ya yi magana a Abuja a wajen kaddamar da kungiyar kamfen din shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Zaben 2019: Muna da tabbacin nasara – Buhari

Zaben 2019: Muna da tabbacin nasara – Buhari
Source: Twitter

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Mista Adams Oshiomhole da ministan sufuri kuma darakta janar na kungiyar kamfen din Buhari, Rotimi Amaechi duk sun hallara.

Sai dai kuma gwamnonin jam’iyyar APC ba su halarci taron ba, koda dai Oshiomhole yayi bayanin cewa aikin kamfen ya sha kan gwamnonin a jihohinsu daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kama babbar mota makare da takardun kuri'un zabe a wata jihar kudu

A baya mun ji cewa Abdullahi Adamu, sanata mai wakiltan Nasarawa ta yamma a majalisar dokokin kasar, ya bukaci yan Najeriya da kada su zabi barayin shugabanni.

Sanatan wanda ya bayyana hakan a wajen kamfen din tazarcensa a Nasarawa, hedkwatar karamar hukumar Nasarawa da ke jihar ya buukaci yan Najeriya da su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda a cewarsa zai fitar da Najeriya daga halin da take ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel