Matasa sun wanke titi da sabulu bayan ziyarar El-Rufa'i, hotuna

Matasa sun wanke titi da sabulu bayan ziyarar El-Rufa'i, hotuna

Wasu fusatattun matasa a karamar hukumar Birnin Gwari sun wanke titunan garin jim kadan bayan wata ziyarar da gwamna jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, ya kai a jiya, Laraba.

A cewar matsan, sun yi amfani da ruwa da omo domin wanke 'tsinuwa' da gwamnan ya kawo garin.

Kazalika, matasan sun kona tsintsiya da tutar APC, wata alama dake nuna cewar basa tare da jam'iyyar a zabe mai zuwa, kamar yadda majiyar mu ta rawaito.

Matasa sun wanke titi da sabulu bayan ziyarar El-Rufa'i, hotuna

Matasa sun wanke titi da sabulu bayan ziyarar El-Rufa'i
Source: Facebook

Daga makobciyar jihar Katsina kun ji cewar a kalla mutane 10 ne suka mutu a yammacin ranar Litinin a mabanbantan wurare biyu a jihar.

A yayin da ake zargin wasu 'yan dabar siyasa da kashe mutane 6 yayin wani taron siyasa a karamar hukumar Sabuwa, wasu mutane 4 sun rasa ransu a kan hanyar Kankara zuwa Dutsinma a jihar Katsina.

DUBA WANNAN: Jam'ian kwastam sun kama kwaya ta miliyoyi a Kaduna

An kashe mutanen ne jim kadan bayan kammala wani taron gangami da jam'iyyar APC ta shirya a karamar hukumar Sabuwa.

Ana zargin wasu 'yan bindiga da kashe mutane 4 a kusa da jami'ar gwamnatin tarayya dake Dutsinma (FUDMA).

'Yan bindigar sun kai wa mutanen hari ne yayin da suke dawowa daga bulaguro a kan titin Kankara zuwa Dutsinma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel