Yanzu Yanzu: An kama babbar mota makare da takardun kuri'un zabe a wata jihar kudu

Yanzu Yanzu: An kama babbar mota makare da takardun kuri'un zabe a wata jihar kudu

- Wasu matasa a yankin karamar hukumar Ogoja da ke jihar Cross River, sun gano wata babbar motar haya dauke da takardun kuri’un zabe sun kuma kama direban motan

- An tattaro cewa babbar motar na hanyar kan fita daga jihar ne a lokacin da aka kama ta

Wasu matasa a yankin karamar hukumar Ogoja da ke jihar Cross River, sun gano wata babbar motar haya dauke da takardun kuri’un zabe a ranar Alhamis, 10 ga watan Janairu sannan suka kuma kama direban motan.

An tattaro cewa babbar motar na hanyar kan fita daga jihar ne a lokacin da aka kama ta.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa matasa a garin Ebung da ke jihar ne suka kama babbar motar wacce ke dauke da lambar rijista na jihar Enugu.

Yanzu Yanzu: An kama babbar mota makare da takardun kuri'un zabe a wata jihar kudu

Yanzu Yanzu: An kama babbar mota makare da takardun kuri'un zabe a wata jihar kudu
Source: Depositphotos

Rahoton yace an gano takardun zaben ne a lokacin duba motoci da mambobin tsaro ke yi a babbar titin garin.

An kawo inda wani idon shaida ke cewa a take da aka bude motar, an gano cewa cike yake da wasu takardun zabe da ba a yi amfani dasu ba mallakar karamar hukumar Boki na 2015.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci gabannin zabe

Sauran kayayyakin da aka gano sun hada da kwamfuta da takardu.

An tattaro cewa direban yayi ikirarin cewa da umurnin hukumar INEC yake zarya daga Calabar inda daga nan aka ce ya fito.

Rahoton yace kwamishinan zabe na jihar Cross River, Frankland Briyai, yayi bayanin cewa an sanar dasu bayanai game da lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel