Yawan kudin da in ka dauka to kurkuku zaka je shekaru ukku - EFCC

Yawan kudin da in ka dauka to kurkuku zaka je shekaru ukku - EFCC

- EFCC tayi karin haske kan daukar kudi ba bisa kaida ba

- $10,000 ko N5,000,000 ne laifi in aka gani a hannu

- A 2011 aka yi dokar don hana manyan lafiuka

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka
Source: Twitter

A kokarin gwamnatin Tarayya na takaita muggan laifuka wadanda sai da kudi tsababa ake tafka su, hukumar hana tu'annati da kassara aikin gwamnati, EFCC, tayi karin haske kan yawan kudin da in mutum yayi hada-hada dasu zai fuskanci hushin hukuma.

Dokar Money Laudering dai, wadda aka iyar a 2011, ta haramta mu'amala da kudi da suka haura N5m ko $10,000 a hannu tsababa, ba tare da an mika su ta banki ba.

Kudaden, muddin aka kama su a hannun mutum zasu jawo masa daurin shekaru uku, ko tara N10,000,000, ko ma dukka biyun.

GA WANNAN: Mahaifin budurwa da tayi ridda ta tsere daga Saudiyya na neman ta ruwa a jallo, sai dai duniya tayi masa caa

Wasu lokutan dai, akan ga 'yan kasuwa musamman gwamnoni da kudi tsababa a hannu ko a akwatuna suna rabo, ko suna amsa, ko don cin hanci ko raba wa masu biyayya, wannan dai ya taka doka, sai dai dokar kasar kamar iya talaka ta tsaya wa, domin kuwa su suna da kariya a doka, wadda ake kira immunity, su kuwa suka sanya wa kansu wannan kariya suka zartas.

A yanzu dai, $10,000 ta kama N3,600,000 kenan, wannan ma na nufi duk hada hada da ta kai haka sai an saka kudin a banki, wannan ne zai hana a dinka fashi da makami, ta'addanci, garkuwa da mutane, kwangilar kisa, da ma sayen kuri'u.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel