Sojoji sun yi murna bayan ragargazar 'yan Boko Haram a Baga

Sojoji sun yi murna bayan ragargazar 'yan Boko Haram a Baga

- Dakarun sojin Najeriya na 707 special forces Brigade sun yiwa Boko Haram mummunar illa a wani artabu da su kayi a garin Baga

- Mai magana da yawun sojin Najeriya, Brig. Janar SK Usman ya ce wasu daga cikin 'yan ta'addan sunyi yunkurin kai farmaki sasanin soji da ke Monguna amma sojojin suka kashe wasu daga cikinsu kuma suka kwata makamai

- Usman ya ce sojojin suna cike da kuzari kuma tuni sun hade da sauran sojojin da ke Baga inda suka fatataki 'yan ta'addan da ke kusa da sansanin sojojin ruwa da kewaye

Kungiyar Boko Haram da ke da alaqa da ISWAP sun rasa 'ya'yan kungiyarsu masu yawa sakamakon artabu da su kayi da dakarun soji na sabuwar runduna ta musamman na NASFC karkashin Operation Lafiya Dole.

Mai magana da yawun sojin Najeriya, Brig. Janar SK Usman ya ce dakarun sojin na 707 Special Forces Brigade sun ragargaji 'yan ta'addan inda suka kashe wasu da dama a hanyar Baga duk da gargadin da akayi musu.

Sojoji sun yi murna bayan ragargazar 'yan Boko Haram a Baga

Sojoji sun yi murna bayan ragargazar 'yan Boko Haram a Baga
Source: Facebook

DUBA WANNAN: 2019: Wani babban basaraken arewa ya yi barazanar tsinewa 'yan siyasa

Sojoji sun yi murna bayan ragargazar 'yan Boko Haram a Baga

Sojoji sun yi murna bayan ragargazar 'yan Boko Haram a Baga
Source: Facebook

"Dakarun sojin na musamman sun atisayen fatatakar 'yan ta'addan ne a ranar 28 ga watan Disambar 2018 inda suka fara da garin Zare, Gudumbali, Kukawa da Cross Kauwa ba tare da sunyi artabu da 'yan ta'addan ba.

"Sai dai a Cross Kauwa, wasu 'yan ta'addan ISWAP sunyi yunkurin tunkurar sojojin hakan yasa sojojin kawar da su sannan suka kwato wasu makamai," inji Kakakin rundunari sojin.

Sojoji sun yi murna bayan ragargazar 'yan Boko Haram a Baga

Sojoji sun yi murna bayan ragargazar 'yan Boko Haram a Baga
Source: Facebook

Sojoji sun yi murna bayan ragargazar 'yan Boko Haram a Baga

Sojoji sun yi murna bayan ragargazar 'yan Boko Haram a Baga
Source: Facebook

"Duk da cewa wasu 'yan ta'addan sunyi yunkurin kai hari a sansanin soji da ke Munguna, dakarun sojojin sunyi musu dabara inda suka kewaye su suka kashe wasu da dama cikinsu kuma suka kwato bindigu da wasu makamai."

Ya ce sojojin suna cike da kuzari kuma tuni sun hade da sauran dakarun sojojin da ke Baga inda za su cigaba kakabo sauran 'yan ta'addan da ke sansanin sojojin ruwa da kewaye.

Sai dai a sakamakon artabun, sojoji guda biyu sun rasu sannan wasu guda biyar sun jikkata.

"An dauke gawar dakarun sojin da suka rasu sannan an garzaya da wadanda suka samu rauni zuwa asibiti domin basu kulawa da ya dace. Sojojin suna cigaba da kakabo sauran 'yan ta'addan da su kayi saura a Arewacin Borno musamman yankin Tafkin Chadi," inji Usman.

Sojoji sun yi murna bayan ragargazar 'yan Boko Haram a Baga

Sojoji sun yi murna bayan ragargazar 'yan Boko Haram a Baga
Source: UGC

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel