Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci gabannin zabe

Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci gabannin zabe

- Shugaba Buhari ya nada Umar Ibrahim El-Yakub a matsayin babban mai bahi shawara akan harkokin majalisar dokokin kasar (majalisar wakilai)

- El-Yakub zai maye gurbin Kawu Samaila wanda yayi murabus daga matsayinsa

- An tattaro cewa Samaila yayi murabus ne domin ya tsaya takara a zabe mai zuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Umar Ibrahim El-Yakub a matsayin babban mai bahi shawara akan harkokin majalisar dokokin kasar (majalisar wakilai).

Nadin na kunshe ne a wani jawabi da mai ba shugaban kasa shawara na musamman a kafofin watsa labarai, Femi Adesina biyo bayan murabus da Kawu Sumaila yayi a matsayin ai ba shugaban kasar shawara a harkokin majalisa (majalisar wakila).

Yanzu Yanzu: Buhari yi sabon nadi mai muhimmanci gabannin zabe

Yanzu Yanzu: Buhari yi sabon nadi mai muhimmanci gabannin zabe
Source: Facebook

Kawu, wanda aka nada a matsayin mai a sugaban kasar shawara a watan Augustan2015, ya yi murabus don yin takarar kujerar da majalisamai wakiltan Sumaila/Takai a majalisar dokokin tarayya a jihar Kano karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Magajinsa, El-Yakub jigon AC daga jihar Kano, ya kasance mamba a majalisar wakilai a 1993 zuwa 2007.

KU KARANTA KUMA: Sarkin Lafia Isa Mustapha Agwai ya rasu yana da shekaru 84

A wani rahoto na daban, mun ji cewa Abdullahi Adamu, sanata mai wakiltan Nasarawa ta yamma a majalisar dokokin kasar, ya bukaci yan Najeriya da kada su zabi barayin shugabanni.

Sanatan wanda ya bayyana hakan a wajen kamfen din tazarcensa a Nasarawa, hedkwatar karamar hukumar Nasarawa da ke jihar ya buukaci yan Najeriya da su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda a cewarsa zai fitar da Najeriya daga halin da take iki, jaridar Punch ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel