EFCC tayi ram da mai gadin ATM da aka ga N30,000,000 a asusunsa

EFCC tayi ram da mai gadin ATM da aka ga N30,000,000 a asusunsa

- Hukumar yaki da rashawa ta gurfanar da wasu gaban kuliya

- Laifukan su sun hada da almundahanar kudade, cin amana da damfara

- Mai shari'a Khobo zai cigaba da sauraron shari'un a wata na gaba

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka
Source: UGC

Hukumar yaki da rashawa, reshen jihar Kaduna ta gurfanar da wani mutum mai suna Alfa Ibrahim gaban mai shari'a Darius Khobo na babban kotun dake jihar akan zargin shi da laifin rashin gaskiya na mallakar Naira miliyan 30 a asusun shi na bankin Ja'iz a ranar talata.

Ibrahim wanda ke kula da ATM din bankin ana zargin shi amfanin kanshi da Naira N33,810,000 da bankin suka zubawa na'urar.

Karar itace kamar haka: "Cewa kai Alfa Ibrahim, a matsayin mai kula da na'urar ATM ta bankin Ja'iz na reshen Kaduna, kamar yanda kotu ta bincika,ta gano cewa kayi rashin gaskiya ta hanyar kwashe Naira 33,810,000 mallakin bankin ba tare da amincewar su ba da kuma niyyar mallake su. A don haka ne kayi laifin da yaci karo da sashi na 270 na dokar Panel Code ta jihar Kaduna kuma abin hukuntawa karkashin sashi na 271 na wannan dokar."

Yaki amsa laifin shi.

Lauya mai kare masu kara, Esmond Garba ya roki kotu da ta sanya wata rana don cigaba da sauraron shari'ar sannan kuma a cigaba da tsare wanda ake kara a gidan kaso.

A yayin da aka daga sauraron shari'a zuwa 14 ga watan Fabrairu, mai shari'a Khobo ya bada beli akan Naira miliyan goma da kuma tsayayye guda daya mazaunin cikin birnin Kaduna.

GA WANNAN: Mahaifin budurwa da tayi ridda ta tsere daga Saudiyya na neman ta ruwa a jallo, sai dai duniya tayi masa caa

Kamar Alfa Ibrahim, shim Muhammad Nalami an gurfanar dashi gaban mai shari'a Khobo akan laifukan hadin kai gurin aikata laifi da kuma cin amana da damfara har ta Naira miliyan 17 mallakin Niroy Nigeria Limited.

Ana zargin Nalami da hada kai da Hafeez Adamu wajen karbar Naira miliyan 17,054,000 daga kamfanin don samar musu da hatsi, amma suka kasa. Yunkurin karbar kudin ya tashi a tutar babu.

Yaki amsa laifin shi.

Mai shari'a Khobo ya daga sauraron karar zuwa 14 ga watan Fabrairu tare da bada umarnin cigaba da tsare shi a gidan yari.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel