Zan kammala dukkanin ayyuka kafin na sauka daga kujera ta - Gwamnan jihar Legas Ambode

Zan kammala dukkanin ayyuka kafin na sauka daga kujera ta - Gwamnan jihar Legas Ambode

- Gwamna Ambode ya ce zai jajirce wajen kammala ayyukan sa gabanin sauka daga kujerar mulki

- Gwamnan na jihar Legas ya yi rarrashi kan fargabar al'ummar sa na barin ayyuka ba tare da kammala su ba

- Ya ce su sha kurumin su dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC Sanwo-Olu ba zai kunyata su ba

Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, yammacin jiya na Laraba ya yi karin haske dangane da fargabar al'ummar jihar sa akan muhimman ayyuka da ke cigaba da gudana yayin da babban zaben kasa ya gabato.

Ambode ya ce gwamnatin sa na ci gaba da yunkuri gami da fafutikar kammala dukkanin ayyukan da ke ci gaba da gudana gabanin karkarewar wa'adin sa bisa kujerar mulki a ranar 27 ga watan Mayu na wannan shekara.

Gwamnan ya yi wannan kira ne na bayar da tabbaci yayin ziyarar shawagi ta ganewa idanun sa wasu muhimman ayyuka da ke ci gaba da gudana cikin wasu sassa na jihar.

Zan kammala dukkanin ayyuka kafin na sauka daga kujera ta - Gwamnan jihar Legas Ambode

Zan kammala dukkanin ayyuka kafin na sauka daga kujera ta - Gwamnan jihar Legas Ambode
Source: Depositphotos

Gwamnan ya ke cewa, a halin yanzu al'ummar jihar su sha kurumin su kan batun kammala ayyukan domin kuwa dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC, Mista Babajide Sanwo-Olu, ba zai kunyatar da su ba.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, gwamna Ambode na ci gaba da gwangwajr jihar Legas ta fuskar ci gaba musamman bunkasa da habakar tattalin arziki.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa kwazon gwamna Ambode da cewa, jihar sa ta yiwa sauran jihohin Najeriya fintinkau a fannin ci gaba ta kowace fuska.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel