Duba matakan da zaka bi domin yin rejistar 2019 UTME - JAMB

Duba matakan da zaka bi domin yin rejistar 2019 UTME - JAMB

Hukumar da ke kula da zana jarabawar share fagen shiga manyan makarantu na gaba da sakandire (JAMB) ta fara sayar da takardar cike gurbin karatu a manyan makarantu, a zango na 2019 (UTME).

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa, da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter @JAMBHQ.

Ga hanyoyi 6 da dalibai zasu bi don yin rijistar jarabawar.

1. Babu wani dalibi da aka yarje mashi ya yaje wata cibiyar zana jarabawar (CBT) ba tare da ya fara kirkirar shafinsa na kansa a shafin yanar gizo na hukumar ba.

KARANTA WANNAN: Sanata Shehu Sani: Babu wani abun kirki da El-Rufai ya tsinanawa Kaduna

Duba matakan da zaka bi domin yin rejistar 2019 UTME - JAMB

Duba matakan da zaka bi domin yin rejistar 2019 UTME - JAMB
Source: Depositphotos

2. An shawarci dalibai su kirkiri shafikansu ta hanyar aika sakon karta kwana, mai dauke da suna (sunan farko, suna na biyu da suna na tsakiya) zuwa ga lamba: 55019

3. Bayan an aika wannan sako, a dan jira na wani lokaci, za a samu sako ya shigo, mai dauke da lambobi 10 a jiki, lambobin ne mabudin shafin dalibi.

4. Za a yi amfani da wadannan lambobi (code) guda 10 da aka turo wajen sayen takardar neman gurbin karatun a wuraren da akaje sayen takardar, walau bankuna, MMOs, MFBs, da dai sauransu.

5. Bayan sayen wannan takarda, za a aikawa dalibi sako a wayarsa, mai dauke da wasu lambobin sirri na bude takardar gurbin karatun (e-pin).

6. Dalibi zai gabatar da wadannan lambobin sirri (e-pin) a cibiyar da aka amince a zana jarabawar JAMB mafi kusa da kai, don yin rejista kai tsaye.

Haka zalika JAMB ta samar da sunaye da adireshin dukkanin cibiyoyin zana jarabawar data amince da su a fadin kasar. Dalibai su duba shafin hukumar na yanar gizo don ganin cikakken sunayen cibiyoyin da ke mafi kusa da su.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel