Kada ku zabi barayin shugabanni, ku zabi Buhari – Adamu

Kada ku zabi barayin shugabanni, ku zabi Buhari – Adamu

- Abdullahi Adamu, sanata mai wakiltan Nasarawa ta yamma a majalisar dokokin kasar, ya bukaci yan Najeriya da kada su zabi barayin shugabanni.

- Sanatan ya bukaci yan Najeriya da su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda a cewarsa zai fitar da Najeriya daga halin da take ciki

- Hakazalika, Mista Abdullahi Sule, dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Nasarawa ya bukaci masu zabe da su guje ma duk wani yaudara don su siyar da katin zabensu ga yan siyasa masu son zuciya

Gabannin zaben 2019, Abdullahi Adamu, sanata mai wakiltan Nasarawa ta yamma a majalisar dokokin kasar, ya bukaci yan Najeriya da kada su zabi barayin shugabanni.

Sanatan wanda ya bayyana hakan a wajen kamfen din tazarcensa a Nasarawa, hedkwatar karamar hukumar Nasarawa da ke jihar ya buukaci yan Najeriya da su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda a cewarsa zai fitar da Najeriya daga halin da take iki, jaridar Punch ta ruwaito.

“A shekaru uku da gwamnatin APC ta yi mulki, mun ga sauyi sosai ta fannin ci gaba a yankunan ababen more rayuwa da ci gaba mutane,” inji shi.

Kada ku zabi barayin shugabanni, ku zabi Buhari – Adamu

Kada ku zabi barayin shugabanni, ku zabi Buhari – Adamu
Source: Twitter

Hakazalika, Mista Abdullahi Sule, dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Nasarawa ya bukaci masu zabe da su guje ma duk wani yaudara don su siyar da katin zabensu ga yan siyasa masu son zuciya.

KU KARANTA KUMA: Babu gwamnonin APC a wurin kaddamar da kwamitin kamfen din Buhari

Sule ya yi wannan kiran ne a Lafia a ranar Talata a wajen gangamin tawagar kamfen din dan takarar shuban kasa na APC a arewa maso tsakiya.

Ya kuma bukaci mazauna jihar da suka isa yin zabe amma basu karbi katin zabensu ba da su ziyarci ofishoshin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) domin su karbi katinsu don su samu damar zaban dan takarar da ransu ke so.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel