Tinubu: Don ka ajiye kudi a tebur yanzu babu wanda zai dauka – Shehu Sani

Tinubu: Don ka ajiye kudi a tebur yanzu babu wanda zai dauka – Shehu Sani

Idan ba ku manta ba kwanan nan ne Asiwaju Bola Tinubu, wanda zai jagoranci yakin neman zaben Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa yake tare da shugaban kasar a babban zabe mai zuwa.

Tinubu: Don ka ajiye kudi a tebur yanzu babu wanda zai dauka – Shehu Sani

Shehu Sani yace kudin Najeriya ya tabarbare a halin yanzu
Source: Depositphotos

A cewar babban Jigon na Jam’iyyar APC, shugaba Buhari mutum ne mai amana, wanda idan aka ajiye kudi a hannun sa za a dawo a iske yadda aka bar su. Wannan magana ta jawo surutu har ta sa Shehu Sani ya tofa albarkacin bakin sa.

Sanatan na yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani yayi amfani da shafin sa na Twitter inda ya caccaki kalaman babban ‘dan siyasar yana mai cewa a wannan mara da ake ciki, ko mutum ya ajiye kudi, yayi tafiyar sa, babu wanda zai dauka.

KU KARANTA: Babu gwamnonin APC a wurin kaddamar da kwamitin yakin zaben Buhari

Fitaccen ‘Dan majalisar ya nuna cewa a wannan lokaci,, Naira ba ta da wani darajar kirki da kimar a zo a gani domin kuwa kudin kasar bai iya sayen wani abin kirki. Shehu Sani yace idan ka ajiye kudin Najeriya a teburi babu wanda zai taba.

‘Dan majalisar ya saba yin shagube a kaikaice ta shafukan sa na sada zumunta na zamani. Yanzu haka Sanatan ya gargadi tsohon shugaban jam’iyyar PDP watau Dr. Ahmad Adamu Muazu ya guji sauya-sheka daga jam’iyyar adawar zuwa APC.

Jam’iyyar PDP dai ta ji haushi kwanaki da Tinubu yace yana bin Muhammadu Buhari ne saboda irin tsabar gaskiyar sa, wanda a cewar sa, Atiku Abubakar bai da ita. PDP tace maganar ace shugaban kasar yana da wata gaskiya labari ne kurum.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel