Barayi sunyi kutse a ofishin Remi Tinubu, sun tafka sata

Barayi sunyi kutse a ofishin Remi Tinubu, sun tafka sata

Rahoton da muka samu ya bayyana cewa wasu barayi sunyi kutse cikin ofishin sanata mai wakiltan mazabar Legas ta tsakiya, Remi Tinubu.

Sanarwar da ta fito daga hannun hadimin sanatan, Nifemi Aje ta ce an gano cewar anyi satar ne a ranar Laraba yayin ma'aikata suka hallara ofishin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A cewar Aje, barayin sun lalata na'urar daukan bidiyo na CCTV sannan suka sace wasu kayayaki masu muhimmanci.

Ya ce tuni an sanar da 'yan sandan da ke aiki a majalisar kuma a halin yanzu ana jiran sakamakon binciken jami'an tsaron.

Barayi sunyi kutse a ofishin Remi Tinubu, sun tafka sata

Barayi sunyi kutse a ofishin Remi Tinubu, sun tafka sata
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda wata matar aure ta shirya sace kanta da kanta a jihar Neja

"Kayayakin da aka sace sun hada da Kumfuta kirar HP, na'urar intanet na Smile, akwatin daukan faifan bidiyo na CCTV da kuma wasu takardu da suka shafi wasu kudirorin doka na tarayya," inji sanarwar.

"An ga alamar sahun mutane a dadumar ofishin. An kuma birkita dirowa na bango da ke ofishin.

"Mun riga mun shigar da kara wurin 'yan sanda kuma sun tabbatar mana cewa an fara gudanar da bincike a kan lamarin.

"Ba mu san wadanda su kayi wannan satar ba ko kuma wanda suka dauki nauyin su.

"A halin yanzu dai muna jirar sakamakon binciken 'yan sanda ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel