Bayan su Shehu Sani sunyi wa El-Rufai 'buqulu' shi kau Bindow bankin duniya ya bashi biliyoyi

Bayan su Shehu Sani sunyi wa El-Rufai 'buqulu' shi kau Bindow bankin duniya ya bashi biliyoyi

- Jihar Adamawa zata amfana da tallafin da bankin duniya ya fitar na dala miliyan 6.7 dan ceto rayukan al'umma

- Kwamishinar lafiya ta jihar ita ta bayyanawa manema labarai hakan

- Wannan kudi yana daga cikin dala miliyan 500 da bankin ya warewa Najeriya

Bayan su Shehu Sani sunyi wa El-Rufai 'buqulu' shi kau Bindow bankin duniya ya bashi biliyoyi

Bayan su Shehu Sani sunyi wa El-Rufai 'buqulu' shi kau Bindow bankin duniya ya bashi biliyoyi
Source: Depositphotos

Jihar Adamawa ta shiga cikin jerin wadanda zasu amfana da tallafin da bankin duniya ya fitar na dala miliyan 6.7 dan ceto rayukan al'umma.

Dr Fatima Abubakar ministan lafiya ta jihar ce ta bayyanawa manema labarai hakan a ranar Alhamis a yayin da take hira dasu a Yola.

Mrs Abubakar tace anyi duba bisa ga takaddunsu anga sun cancanta kafin a sanyasu cikin wannan shiri.

Tace bankin duniya tare da hadin gwiwar hukumar lafiya ta kasa sunyi duba na tsanaki akan hakan.

DUBA WANNAN: An haramta amfani da mayukan bilicin masu haskaka fata a kasar Rwanda

Inda sakamako ya nuna cigaban da aka samu a jihar a shekara ta 2018.

Ta kara da cewa sakamakon ya nuna yanda jihar ta fara gudanar da wannan shiri nata kamar yanda aka tsara.

Tace wannan dala miliyan 6.7 din yana daga cikin dala miliyan 500 da bankin ya warewa Najeriya.

Gudummawar da gwamnoni ke nema, na iya zama bashi da bassu iya biya, wasu lokutan kuwa, taimakon jin kai ne da duniya ke baiwa inda talauci yayi katutu.

Yankin arewa maso gabas dai, na fama da talauci wanda masu kokarin kafa daular Islama ke ta faman rushe wa shirin kyautata rayuwa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel