An yiwa tsohon shugaban kasa Mugabe satar kudi na $150,000 a kasar Zimbabwe

An yiwa tsohon shugaban kasa Mugabe satar kudi na $150,000 a kasar Zimbabwe

- Wata 'yar uwa ga tsohon shugaban kasar Zimbabwe, ta kitsa kuntungwilar yiwa dan uwan ta satar makudan kudi

- Constancia Mugabe da sauran miyagun biyu sun yashe dalar Amurka 150,000 mallakin tsohon shugaban kasar

-Sun yi bushashar su ta sayen kadarori na more rayuwa inji jami'i mai shigar da kara a gaban kotu

An yiwa tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, aika-aika ta satar makudan kudi na dalar Amurka 150,000 cikin wata jakar sa ta ajiya kamar yadda wata babbar kotun kasar dake zamanta a birnin Harare ta zayyana.

Kotun ta ce ababen zargin uku da suka aikata wannan mummunar ta'ada, sun yi bushashar su ta sayen dabbobin kiwo, gidaje da kuma motoci na more rayuwa kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Ababen zargi da suka hadar har da wat 'yar uwa ta tsohon shugaban kasa, Constacia Mugabe mai shekaru hamsin a duniya, a jiya Laraba sun gurfana gaban wata babbar kotun majistire ta Chinhoyi kamar yadda kafofin watsa labarai na kasar suka ruwaito.

Tsohon shugaban kasar Zimbabwe; Robert Mugabe

Tsohon shugaban kasar Zimbabwe; Robert Mugabe
Source: Depositphotos

Constancia Mugabe ta ribaci kusancin ta da tsohon shugaban kasar, inda ta kitsa kutungwilar yashe dukiyar dan uwan ta a gidansa na kauye tun a watan Dasumba na shekarar 2018 da ta gabata.

Teveraishe Zinyemba, jami'i mai shigar da kara a gaban kotu ya bayar da shaidar cewa, daya daga cikin ababen zargin, Johanne Mapurisa ta yi bushashar ta wajen sayen Mota ta alfarma kirar Toyota Camry da kuma sayen wani katafaren gida na dalar Amurka Dubu Ashirin.

Ita ko dayar mai zuciyar dan bera, Saymore Nhetekwa, ta yi bushashar ta gami da wadaka wajen sayen mota kirar Honda da kuma sayen dabbobin kiwo da suka hadar da shanu da Aladu kamar yadda jami'i Zinyemba ya bayyana.

KARANTA KUMA: Cunkoson gidajen yari: Zan haramta kama masu laifi - Lauyan Kolu na jihar Nasarawa ya gargadi hukumar 'yan sanda

Kotun ta bayar da belin ababen zargin tare daga sauraron karar su zuwa ranar 24 ga watan Janairu. Sai dai kawowa yanzu hukumar 'yan sanda ta bazama wajen neman daya daga cikin miyagun da ke da hannun cikin wannan muguwar aika-aika.

A halin yanzu ba bu wata masaniya ta inda tsohon shugaban kasar ya ke tun bayan rahoton da shugaban kasar ya bayyana, Emmerson Mnagagwa, kan cewa Mugabe na jinya a wani asibitin kasar Singapore tun a watan Nuwamba na shekarar bara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel