Dalilin da yasa ya zama wajibi a jinjinawa shugaban kasa Buhari - Sanata Shehu Sani

Dalilin da yasa ya zama wajibi a jinjinawa shugaban kasa Buhari - Sanata Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani ya jinjinawa Buhari bisa bayyana kudirinsa na cewar ba zai yi amfani da ko kwabon kudin gwamnati ba, wajen yakin zabensa a 2019

- A ranar Laraba, Buhari ya sha alwashin cewa ba zai ciri koda kwandala daga baitul malin gwamnati ba da sunan daukar nauyin yakin zaben sa a karo na biyu

- Sai dai Sanata Shehu Sani, ya gargadi gwamnonin da ke baiwa shugaban kasar tallafin ababen hawa don yakin zabensa, da su yi hattara

Shehu Sani, sanatan da ke wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai, ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa bayyana kudirinsa na cewar ba zai yi amfani da ko kwabon kudin gwamnati ba, wajen yakin zabensa a 2019.

A ranar Laraba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa ba zai ciri koda kwandala daga baitul malin gwamnatin tarayya ba da sunan wai ya dauki nauyin yakin zaben sa a karo na biyu.

Shugaban kasar ya dauki alkawarin ne a cikin wata sanarwa daga Malam Garba Shehu, babban mai tallafa masa ta fuskar sadarwa da watsa labarai, bayan kammala taron sirri na majalisar zartaswar kasar FEC, a Abuja.

KARANTA WANNAN: Da dumi duminsa: Gwamnatin tarayya za ta ciyo bashin N823bn

Dalilin da yasa ya zama wajibi a jinjinawa shugaban kasa Buhari - Sanata Shehu Sani

Dalilin da yasa ya zama wajibi a jinjinawa shugaban kasa Buhari - Sanata Shehu Sani
Source: UGC

Sani ya yabawa shugaban kasa Buhari kan wannan mataki da ya dauka. Sai dai ya gargadi gwamnonin da ke baiwa shugaban kasar tallafin ababen hawa don yakin zabensa, da su yi hattara.

Dan majalisar dattijan, a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce: "Shugaban kasa Buhari ya cancanci yabo, na zama Shugaban kasa na farko da ya fito karara ya kalubalanci amfani da kudin jama'a wajen yakin zabensa.

"Gwamnonin da sauran masu rike da hukumomi na kasar nan, masu yiwa Buhari kyautar motoci da sunan tallafawa yakin zabensa suyi hattara. Ku ji tsoron hannayenku a lokacin da kuka je ciyar da zaki nama maras gwabi, kar ya hada da hannunku."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel