Kin halaratar taron PDP: Mataimakin gwamna a jihar kudu ya dakatar da albashin manyan jami'an gwamnati

Kin halaratar taron PDP: Mataimakin gwamna a jihar kudu ya dakatar da albashin manyan jami'an gwamnati

- Mataimakin gwamnan Ebonyi, Dr Kelechi Igwe ya dakatar da albashin jami’an gwamnati

- Dr Kelechi Igwe ya yi umurnin haka ne saboda kin halartan taron PDP da jami’an suka yi

- Ya bayyana cewa an shirya taron ne domin masu ruwa a tsaki su samo hanyoyin da za a tabatar da gangamin jam’iyyar cikin nasara a wannan rana

Mataimakin gwamnan Ebonyi, Dr Kelechi Igwe, ya yi umurnin cewa a kwace albashin watan Janairu na wasu jami’an siyasa daga Ikwo, mahaifarsa kan rashin halartan wani taro.

Umurnin da aka bayar a ranar Alhamis, 10 ga watan Janairu, ya nuna cewa jami’an da abun ya shafa basu halarci wani taro da aka shiry don angamin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a yankin ba a ranar 17 ga watan Janairu.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa an shirya taron ne domin masu ruwa a tsaki su samo hanyoyin da za a tabatar da gangamin jam’iyyar cikin nasara a wannan rana.

Kin halaratar taron PDP: Mataimakin gwamna a jihar kudu ya dakatar da albashin manyan jami'an gwamnati

Kin halaratar taron PDP: Mataimakin gwamna a jihar kudu ya dakatar da albashin manyan jami'an gwamnati
Source: Twitter

“Abun ashha, wasu masu rike da mukaman siysa da gangan suka ki halartan taron duk da cewar an sanar da ranar hakan, wuri da kuma lokaci taron.

“Don haka, na umurci babban sakataren gwamna, Cif Clement Nweke, da ya tabbaar da cewa jami’an a abunya shafa sun rasa albashinsu na watan Janairu.

KU KARATA KUMA: Buhari, Osinbajo da sauransu za su halarci babban gangami a Abia

“Wannan doin ya zamo izina ne ga sauran yayinda mutanen Ikwo suke burin ganin sun gudanarwa da PDP gangami mai cike da nasara a wannan rana,” cewar ataimakin gwamnan a wani jawabi daga sakataren labaransa, Mista Monday Uzor.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel