Sunaye: Rundunar soji zata rufe wasu hanyoyi 7 a Abuja ranar 15 ga wata

Sunaye: Rundunar soji zata rufe wasu hanyoyi 7 a Abuja ranar 15 ga wata

Hedikwatar rundunar soji ta kasa (DHQ) ta fitar da sanarwar cewar zata rufe wasu hanyoyi a cikin garin Abuja domin gudanar da bikin ranar tunawa da sadaukarwar jami'an soji (AFRDC) na shekarar 2019 da za a yi ranar 15 ga watan Janairu.

A sanarwar da mataimakin darektan yada labarai na rundunar soji (DDI), Birgediya Janar John Agim, ya fitar ya ce shagulgulan bikin na wannan shekara zasu fara ne ranar Talata, 15 ga watan Janairu, 2019, a garin Abuja da misalin karfe 9 na safe.

A cewar Agim, shagulgulan bikin zasu shafi masu amfani da wasu hanyoyin cikin garin Abuja, musamman da safe. Hanyoyin sune;

1. Kwanar kotun daukaka kara (court of appeal junction)

2. Kwanar ma'aikatar harkokin kasashen waje (Foreign Affairs Junction)

Sunaye: Rundunar soji zata rufe wasu hanyoyi 7 a Abuja ranar 15 ga wata

Kakakin rundunar soji, Birgediya Janar SK Usman
Source: Facebook

3. Kwanar gidan jihar Bayelsa (Bayelsa House Junction)

4. Kwanar gidan jihar Benuwe (Benue House Junction)

5. Gadar sama ta Phase 3 (Phase 3 flyover)

6. Aso Drive by phase 3

DUBA WANNAN: Boko Haram sun bawa garuruwa biyu a Borno wa'adi

7. Mopol gate behind National Arcade

"Muna bawa jama'a hakuri a kan wannan rufe wadannan hanyoyi na wucin gadi. Muna kira ga jama'a su jama'a da su hada kai da jami'an soji domin tunawa da dakarun da suka sadaukar da rayuwar su domin kare kasar mu," a jawabin Agim.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel