Yan bindiga sun bindige jami’in FRSC har lahira a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Yan bindiga sun bindige jami’in FRSC har lahira a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Matsalar tsaro a Najeriya ya zama abinda ya zama, inda za ka ga sai an yunkura an magance na wani bangare, sai kaga matsalar ta kunno kai a wani bangare da sabon salo, kuma sai ana murna bako ya tafi, ashe mugun yana bayan gari.

Wasu gungun yan bindiga da suka dade suna addabar babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja sun bindige wani jami’in hukumar kare haddura ta kasa, FRSC a ranar Laraba 9 ga watan Janairu yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna.

KU KARANTA: An yanka ta tashi: Shuwagabannin Inyamurai sun yi fatali da takarar Atiku Abubakar

Yan bindiga sun bindige jami’in FRSC har lahira a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja
Source: Depositphotos

Kwamishinan Yansandan jahar Kaduna, Abdulrahman Ahmad ne ya sanar da haka a ranar Alhamis 10 ga watan Janairu, inda yace yan bindigan sun tare da motar jami’in ne a ranar Laraba, inda suka bude masa wuta, tare da wani fasinja dake cikin motarsa.

Majiyar Legit.com ta ruwaito jim kadan bayan sun halaka mutanen ne sai yan bindigan suka rankaya cikin daji dake gefen hanyar a guje don gudun kada a cimmasu, a can suka bar mutanen cikin matsananancin hali rai fakwai mutu fakwai.

Ko kafin a kawo musu dauki tuni sun ce ga garinku nan. Sai dai kwamishina Abdulrahman ya danganta cigaba da ruruwar wannan matsala ga wasu baragurbin jami’an tsaro dake taimaka ma yan bindigan da bayanai, da kuma mazauna kauyukan kan hanyar.

Amma duk da haka kwamishina Abdulrahman yace ya dauki alwashin sai ya kama duk masu hannu cikin wanna’a ta’asa, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, ya kara da cewa ba zasu yi kasa a gwiwa ba don tabbatar da an hukunta duk masu hannu cikin lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel