Babu gwamnonin APC a wurin kaddamar da kwamitin kamfen din Buhari

Babu gwamnonin APC a wurin kaddamar da kwamitin kamfen din Buhari

- Gwamnonin jam’iyyar APC sun ki halartan taron kaddamar da kungiyar kamfen din shugaba Buhari

- An nada gwamnonin a matsayin mambobin kungiyar domin suyi jagoranci a jihohinsu

- Shugaba Buhari ne ke jagorantar taron a fadar shugaban kasa da ke Abuja

Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun ki halartan taron kaddamar da kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar wanda shugaban kasa Muhamadu Buhari ke jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

An nada gwamnonin a matsayinmambobin kungiyar domin suyi jagoranci a jihohinsu.

Babu gwamnonin APC a wurin kaddamar da kwamitin kamfen din Buhari

Babu gwamnonin APC a wurin kaddamar da kwamitin kamfen din Buhari
Source: UGC

Amma a lokacin da kungiyar ke gudanar da taronta na farko, wanda ake sanya ran shine zai nuna manufofin kamfen din a ranar Alhamis, sai aka nemi gwamnonin ko sama ko kasa aka rasa a wajen taron.

Sai dai kuma, jiga-jigan APC da dama ciki harda babban jigon jam’iyyar na kasa Asiwaju Bola Tinubu wanda shine aka baiwa wuka da nama na kamfen din da kuma shugaban jamiyyar na kasa, Adam Osiomhole sun hallara.

KU KARANTA KUMA: Kisan Janar Alkali: Rundunar 'yan sanda ta bayyana neman wasu mutane 13 ruwa a jallo

A halin da ake ciki mun sam labarin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin shuaban kasa Yemi Osinbajo da shugaban jam’iyyar All progressive Congress, Adams Oshiomhole, za su je Umuahia, babbar birnin jihar Abia, don kaddamar da kamfen din shugaban kasa na APC da gwamna wanda za a gudanar a ranar Juma’a.

Daraktan kwamitin gangamin APC na jihar Abia, Cif Acho Obioma wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, yace jam’iyyar za ta yi amfani da wannan dama wajen yin jawabi game da shirinta na kwace mulki a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel