Obi Ezekwesili na ci gaba da ragadinta kasuwanni da gidaje

Obi Ezekwesili na ci gaba da ragadinta kasuwanni da gidaje

- Ezekwesili ta kai ziyara kasuwar Abuja, tayi alkawarin samar da cigaba a bangaren tatalin arziki.

- ACPN zata maids hankali wajen kawo canji a bangaren Ilmi da tattalin arziki.

Tayi kira a zabi jam'iyyar ACPN a babban zabe me zuwa

Obi Ezekwesili na ci gaba da ragadinta kasuwanni da gidaje

Obi Ezekwesili na ci gaba da ragadinta kasuwanni da gidaje
Source: UGC

'Yar takarar shugabancin kasar nan a tutar jam'iyar ACPN Dr Obiageli Ezekwesili ta kai ziyara kasuwar Mararraba da Nyanya a ranar larabar data gabata inda ta bayyana manufofin yakin neman zaben ta.

Akwai dai 'yan takara irinta da Kingsley Moghalu, da ma Jerry Gana, wadanda masu neman labarai basu fiye bibiya ba, ganin cewa ba'a san jam'iyyarsu ba. Su kau,sun ci gaba da yakin neman zabe, dama cewa sun tabbatar jama'a zasu zabe su.

GA WANNAN: Takaddama a Faransa bayan an bude wani Masallaci da ake kira 'na-kowa'

Mrs Obi, wadda ta taba yin Ministar Ilimi, da ma aiki a bankin duniya, ta daukii alkawarin tallafawa 'yan kasuwa da masu kananun sana'o'i a yunkurin da zatayi na kawo canji a bangaren tattalin arzikin talakawa.

Tace da zarar taci zabe to hakika diyan 'yan kasuwar zasu samu Ilmi kyauta a dalilin fahimtar da tayi cewa yawancin 'ya'yansu basu samun damar zuwa makaranta sakamakon yawon talla da suke yi a dai-dai lokutan zuwa makaranta.

Cibiyar yada labarai ta kasa dai ta rawaito cewa Ezekwesili ta taka rawa sosai da 'yan kasuwar a lokacin da take bayanin manufofin nata.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel