Da dumi duminsa: Gwamnatin tarayya za ta ciyo bashin N823bn

Da dumi duminsa: Gwamnatin tarayya za ta ciyo bashin N823bn

Gwamnatin tarayya za ta ciwo bashin N823bn daga bangaren tattalin arzikin cikin gida a cikin watanni hudu na farkon shekarar 2019 (Q1'19) ta hannun kudaden da aka tara na asusun bai daya, wanda babban bankin Nigeria (CBN) zai bayar.

Babban bankin CBN ne ya sanar da cewa gwamnatin tarayya zata ranci akalla N823bn. Bankin ya fitar da bayanin hakan a wani rahoto kan shirinta na kudaden asusun bai daya na watanni hudun farko na shekarar 2019 (Q1'19) da ta fitar a jiya.

Kudaden da za a fitar daga asusun bai daya a watanni hudu na farkon shekarar sun hada da N51.5bn har na tsawon kwanaki 91, sai N23.8bn na tsawon kwanaki 182, sai kuma N607.1bn na tsawon kwanaki 364.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: ASUU ta ce bata cimma wata matsaya da gwamnatin tarayya ba

Da dumi duminsa: Gwamnatin tarayya za ta ciyo bashin N823bn

Da dumi duminsa: Gwamnatin tarayya za ta ciyo bashin N823bn
Source: Depositphotos

Wani nazari da bincike na jaridar Vanguard, ya nuna cewa daga 3 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan, CBN zai saki N555.02bn daga kudin asusun bai daya, da suka hada da N23.8bn na tsawon kwanaki 91, sai N116.16 na tsawon kwanaki 182 da kuma N415.06bn na tsawon kwanaki 364.

A watan Fabreru, babban bankin zai saki N268.7 daga asusun bai daya, da suka hada da N27.8bn na tsawon kwanaki 91, sai N48.8bn na tsawon kwanaki 182 da kuma N192.1bn na tsawon kwanaki 364.

Sai dai yawan kudin da za a cire sabo, daga asusun bai daya ya kai N84.87bn, wanda yake kasa da N907.87 da zai habaka kuma har a mayar da bashin a cikin lokaci, wanda yasa gwamnatin ke kokarin rage yawan cin bashi daga asusun cikin gida, don mayar da hankali ga kasashen waje.

Kudaden da asusun bai dayan zai samu idan suka habbaka, sun hada da N59bn na tsawon kwanaki 91, sai N248.8bn na tsawon kwanaki 182, da kuma N678.1bn na tsawon kwanaki 364.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel