Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace mutane 20 a Katsina

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace mutane 20 a Katsina

- A kalla mutane 20 ne masu garkuwa da mutane suka sace a garin Kankara a Katsina a hanyarsu na komawa gida daga wurin daurin aure

- Mutane da dama daga kauyukan da ke karamar hukumar Safana na jihar ta Katsina sun tabbatar da cewar an sace 'yan uwansu

- Sai dai jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, Gambo Isah ya ce rundunar 'yan sanda ba ta samu labarin afkuwar lamarin ba a lokacin rubuta wannan rahoton

Hankulan al'umma ya tashi a Katsina a yayin da wasu 'yan bindiga suka kai farmaki kan wasu mutane da ke dawowa daga daurin aure a Kankara kuma su kayi awon gaba da mutane 20 daga cikinsu.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace mutane 20 a Katsina

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace mutane 20 a Katsina
Source: Twitter

Premium Times ta ruwaito cewa mazauna wasu kauyuka a karamar hukumar Safana da ke jihar ta Katsina sun tabbatar da cewa 'yan bindigan sun bude musu wuta ne hakan yasa suka tsaya sannan suka kwace musu kudade da wayoyin salula.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kwato manyan bindigu 45 daga hannun 'yan ta'adda a jihar Arewa, hoto

An gano cewa 'yan bindigan sun harbi daya daga cikin mutanen da ya yi kokarin tserewa a hannu, hakan yasa suka saki shi kuma suka nuna masa hanyar ta zata kaishi zuwa babban titi.

A cewar rahoton, mutumin yana asibitin tarayya da ke jihar Katsina inda aka yi masa tiyata aka ciro harsasai biyu a hannunsa.

Tuni dai masu garkuwa da mutanen sun kira mazauna kauyen inda suka bukaci a basu kudin fansa N50 miliyan amma daga baya sun rage zuwa N40 miliyan.

Manyan garin sun ki amincewa da biyan kudin fansar, sun ce garkuwa da mutane ya zama ruwan dare kuma ba za a taba denawa muddin ana biyansu kudin fansar. Sun ce za su rungumi addu'a da fatan Allah ya kubutar da 'yan uwansu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Gambo Isah ya ce rundunar bata samu rahoton afkuwar wannan harin ba a halin yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel