Ko Atiku zai fi samun natsuwa idan ya damka kudinsa hannun Buhari - Osinbajo

Ko Atiku zai fi samun natsuwa idan ya damka kudinsa hannun Buhari - Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya siffanta mai gidansa, shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan siyasa mai gaskiya da rikon amana

- A jawabin da ya yi a wajen yakin neman zabe, Osinbajo ya ce ko Atiku Abubakar ya san cewa Buhari mutum ne mai nagarta

- Osinbajo ya kara da cewa Najeriya tana bukatar jagora ne mai gaskiya da nagarta irin Buhari a shekarar 2019

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce maigidansa, Shugaba Muhammadu Buhari dan siyasa ne mai nagarta, ya kara da cewa dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar yana da masaniya kan nagartar Buhari.

A yayin da ya ke jawabi a wajen taron kamfen da wata kungiyar masu goyon Buhari suka shirya a ranar Talata 8 ga watan Janairu a Abuja, Osinbajo ya ce APC da 'yan Najeriya ba za su bari Atiku da mabarbatarsa abokansa na PDP su dawo kan mulki ba a 2019.

Ko Atiku zai fi samun kwanciyar hankali idan ya damka kudinsa hannun Buhari - Osinbajo

Ko Atiku zai fi samun kwanciyar hankali idan ya damka kudinsa hannun Buhari - Osinbajo
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Sojoji sun kwato manyan bindigu 45 daga hannun 'yan ta'adda a jihar Arewa, hoto

Legit.ng ta gano cewar Osinbajo ya siffanta Buhari a matsayin irin jagora da shugaban da Najeriya ke bukata a shekarar 2019.

Ya ce: "Ba zamu bari su dawo mulki ba. Tambayar da ya dace muyi itace; wane zaka bawa amanar kudin ka?

"Idan ni ne, zan ajiye kudi na a bankin Buhari saboda har makiyarsa sun san cewa shi mai gaskiya ne; har barayin ma sun san shi mutum ne mai nagarta.

"Har makiyarsa ma za su ajiye kudinsu a bankinsa domin sun san babu abinda zai samu kudinsu; muna da shugaban kasa mai nagarta da zaiyi amfani da kudinmu domin ayyukan da aka tanada ayi da kudin.

"Shima Atiku ya san Buhari mutum na mai nagarta; kuma zai taba musunta hakan ba; babu wanda zai musunta haka; wannan shine irin jagoran da muke bukata a kasar mu yanzu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel