An yanka ta tashi: Shuwagabannin Inyamurai sun yi fatali da takarar Atiku Abubakar

An yanka ta tashi: Shuwagabannin Inyamurai sun yi fatali da takarar Atiku Abubakar

Hadaddiyar kungiyar yayan yan kabilar Ibo ta kasa baki daya ta musanta rahoton da ake yadawa a kafafen sadarwar na cewa wai ta zabi dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a matsayin wanda za ta mara ma baya a zaben 2019.

Mataimakin kaakakin kungiyar, Chuks Ibgebu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis 10 ga watan Janairu, a garin Enugu a yayin zantawa da manema labaru don cikar shuwagabannin kungiyar shekara biyu a madafan iko, inda yace basu san da maganar ba.

KU KARANTA: Babban Magana: Buhari ba shi da wata kima, yaki da rashawa karyace – Inji Bukola Saraki

An yanka ta tashi: Shuwagabannin Inyamurai sun yi fatali da takarar Atiku Abubakar

Atiku Abubakar
Source: UGC

s

Ibegbu yace ya zama wajibi su yi karin haske game da wancan rahoto domin jama’a su fahimci su wanene ba wanene ba, musamman game da taron da wasu shugabannin Ibo suka kira a ranar 14 ga watan Nuwambar 2018 inda suka bayyana goyon bayansu ga takarar Atiku.

Kaakakin ya bayyana wannan taro a matsayin taron abokanan Atiku yan kabilar Ibo, kuma Atikun da kansa ya samu halartar wannan taro, haka zalika babban daraktan yakin neman zabensa, Sanata Bukola Saraki ya samu halarta, don haka yace ya kamata jama’a su banbance.

“Dole ne sai mun yi takatsantsan a matsayinmu na kungiya, saboda yayanmu da dama sun bazama a kungiyoyi daban daban, don haka ba daidai bane ace wai kungiyar Ohanaeze Ndigbo tana goyon bayan wani dan takara, wancan taro da aka yi ba mu muka shirya shi ba, abokan Atiku ne suka shirya shi.

“Amma duba da bukatarmu, zamu bayyana goyon bayanmu ga duk wani dan takara da zai sauya fasalin kasar nan gaba daya idan ya zama shugaban kasa, a yan kwanaki masu zuwa zamu bayyana ma duniya matsayinmu game da zaben 2019.” Inji shi.

Da yake tsokaci kan cigaban da aka samu a karkashin jagororin kungiyar Ohanaeze Ndigbo kuwa, Ibegu yace shuwagabannin kungiyar na yanzu sun yi iya bakin kokarinsu wajen hada kawunan kungiyoyin inyamurai daban daban domin zama tsintsiya daya madaurinki daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel