Buhari, Osinbajo da sauransu za su halarci babban gangami a Abia

Buhari, Osinbajo da sauransu za su halarci babban gangami a Abia

- Shugaban kasa Buhari, mataimakin shuaban kasa Osinbajo da shugaban jam’iyyar APC, Oshiomhole, za su je Umuahia, babbar birnin jihar Abia

- Za su ziyarci jihar ne domin kaddaar da kamfen din shugaban kasa da na dan takarar gwamna a jihar a gobe Juma’a

- Daraktan kamfen din APC a jihar shugaba Buhari ya yi ayyukan ci gaba da yawa a yankin kudu maso gabas da zai karfafawa masu gwiwar zabarsa a zabe mai zuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin shuaban kasa Yemi Osinbajo da shugaban jam’iyyar All progressive Congress, Adams Oshiomhole, za su je Umuahia, babbar birnin jihar Abia, don kaddamar da kamfen din shugaban kasa na APC da gwamna wanda za a gudanar a ranar Juma’a.

Daraktan kwamitin gangamin APC na jihar Abia, Cif Acho Obioma wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, yace jam’iyyar za ta yi amfani da wannan dama wajen yin jawabi game da shirinta na kwace mulki a jihar.

Buhari, Osinbajo da sauransu za su halarci babban gangami a Abia

Buhari, Osinbajo da sauransu za su halarci babban gangami a Abia
Source: UGC

Yace shugaba Buhari ya yi ayyukan ci gaba da yawa a yankin kudu maso gabas da zai karfafawa masu gwiwar zabarsa a zabe mai zuwa.

Obioma ya bayyana cewa APC za ta kaddamar da Kamfen a Abia bisa ga kudrin kawo ci gaba a gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Fim din Yaki A Soyayya ya shiga sahun manyan fina-finar 20 a Najeriya

A wani lamari na daban, mun ji cewa, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce maigidansa, Shugaba Muhammadu Buhari dan siyasa ne mai nagarta, ya kara da cewa dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar yana da masaniya kan nagartar Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel