Cunkoson gidajen yari: Zan haramta kama masu laifi - Lauyan Kolu na jihar Nasarawa ya gargadi hukumar 'yan sanda

Cunkoson gidajen yari: Zan haramta kama masu laifi - Lauyan Kolu na jihar Nasarawa ya gargadi hukumar 'yan sanda

- Lauyan kolu na jihar Nasarawa ya yi barazanar haramta kama masu laifi

- Babban masanin shari'ar ya bayyana damuwar sa kan cunkoson fursunoni a gidajen yari

- Ya ce hukumar 'yan sanda ke da bayar da wannan gudunmuwa ta hana ruwa gudu a gidajen kaso

Da sanadin kamfanin dillancin labarai na kasa mun samu cewa, an yiwa hukumar 'yan sanda barazanar daina zartar da hukunci gami da kuma kama masu laifi sakamakon cunkoson miyagu a gidajen kaso da ya yi kamari a jihar Nasarawa.

Lauyan kolu na jihar Nasarawa, Alkali Suleiman Dikko, shine ya yi wannan barazana a jiya Laraba yayin ziyarar sa ta shawagi zuwa gidajen kaso na jihar Nasarawa da ke karkashin kulawar gwamnatin tarayya.

Dikko ya yi wannan barazana ga hukumar 'yan sandan jihar biyo bayan gazawarta na rashin gurfanar da ababen zargi a gaban Kotu domin zartar da hukunci bisa ga tanadi na doka da kuma shari'a.

Cunkuso a gidajen yari

Cunkuso a gidajen yari
Source: UGC

Babban masanin shari'ar ya bayyana takaicin sa gami da mamaki dangane da yadda hukumar 'yan sanda ta gaza wajen gurfanar da ababen zargi a gaban kuliya domin zartar ma su da hukunci daidai da abin da suka aikata.

KARANTA KUMA: Hukumar 'yan sanda ta dakile wani mummunan hari a Zamfara

A cewar sa, ana ci gaba da samun tsaiko da fuskantar kalubalai na rage cunkoson adadin fursunoni a sakamakon gazawar hukumar 'yan sanda da ta ke jibge ababen zargi a gidajen kaso bayan cafke su da tsawon watanni a madadin gurfanar da su a gaban kuliya.

Babban Lauyan ya kuma yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki musamman cibiyar kula da walwala da kum jin dadin fursunoni da ta gaggauta tunkarar wannan lamari a bisa mahanga ta jinkai da kuma tabbatar da adalci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel