Bamu da wuta a gida, siyan ruwan sha muke yi – Dan Dino Melaye ya koka

Bamu da wuta a gida, siyan ruwan sha muke yi – Dan Dino Melaye ya koka

- Sanata Ben Murray-Bruce, dan majalisa mai wakiltan Bayelsa ta gabas a majalisar dokokin kasar, yayi ikirarin cewa yan sanda sun umurci kafanin wutar lantarki na Abuja da kada su mayar da wutar gidan Sanata Dino Melaye

- Babban dan sanatan mai wakiltan Kogi na yamma, Josh Melaye, ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa tunda mahaifinsu ya mika kansa ga hukumar yan sanda a ranar Juma’a, 4 ga watan Janairu, an barsu cikin mawuyacin yanayi

Sanata Ben Murray-Bruce, dan majalisa mai wakiltan Bayelsa ta gabas a majalisar dokokin kasar, a ranar Laraba, 9 ga watan Janairu, yayi ikirarin cewa yan sanda sun umurci kamfanin wutar lantarki na Abuja wato Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) da kada su mayar da wutar gidan Sanata Dino Melaye.

Bamu da wuta a gida, siyan ruwan sha muke yi – Dan Dino Melaye ya koka

Bamu da wuta a gida, siyan ruwan sha muke yi – Dan Dino Melaye ya koka
Source: UGC

Sanata Murray-Bruce ya bayyana hakan ta shafinsa na twitter, @benmurraybruce.

Ya rubuta: “Toh bayan @dino_melaye ya mika kanshi ga hukumar @PoliceNG, rundunar yan sanda ta yi bincike saosai a gidansa sannan kuma ba’a samu komai ba. Duk da haka, yan sandan sun ki bari AEDC su hada wutar kuma. Yanzu haka, yaran Dino na kwana ckin duhu a cikin wani mawuyacin hali."

Da yake maimaita zargin Sanata Murray-Bruce, babban dan sanatan mai wakiltan Kogi na yamma, Josh Melaye, ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa tunda mahaifinsu ya mika kansa ga hukumar yan sanda a ranar Juma’a, 4 ga watan Janairu, an barsu cikin mawuyacin yanayi.

A rubutun da ya wallafa, Josh yya bayyana cewa basu da wuta a gidansu sannan kuma cewa kanansa na siyan ruwan sha ne. Ya kuma yi zargin cewa yan sanda sun hana baki ziyartarsu.

KU KARANTA KUMA: PDP ta rasa mambobinta 450 a Akwa Ibom

Ga yadda ya rubuta a kasa:

Bamu da wuta a gida, siyan ruwan sha muke yi – Dan Dino Melaye ya koka

Bamu da wuta a gida, siyan ruwan sha muke yi – Dan Dino Melaye ya koka
Source: UGC

Sanata Dino Melaye dai ya mika kansa ga yan sanda mayan kwanaki takwas da suka yi suna mamaye da gidan nasa da ke birnin tarayya Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Leit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel