Hukumar 'yan sanda ta dakile wani mummunan hari a Zamfara

Hukumar 'yan sanda ta dakile wani mummunan hari a Zamfara

Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara, ta samu nasarar dakile wasu munanan hare-hare da masu tayar da zaune tsaye suka shirya zartar wa kan wasu yankunan al'umma da ke jihar kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar ta kuma samu nasarar cafke wani kasurgumin dan ta'adda da ake zargin sa da shahara kan tanadar da makamai ga dukkanin masu tayar da zaune a fadin jihar.

Alhaji Muhammadu Zannah, kwamishinan 'yan sanda na jihar, shine ya bayar da shaidar hakan a jiya Laraba yayin ganawar sa da manema labarai cikin babban birnin jihar na Gusau.

Hukumar 'yan sanda ta dakile wani mummunan hari a Zamfara

Hukumar 'yan sanda ta dakile wani mummunan hari a Zamfara
Source: Depositphotos

Zannah ya bayyana cewa, hukumar 'yan sandan ta samu nasarar warware kutungwilar wasu munanan hare-hare da ma su muguwar ta'adda suka kudirci zartar wa a kauyukaan Dan-Gamji, Bindin, Goburawa da kuma Chali da ke karkashin masarautar Dan Sadau a karamar hukumar Maru ta jihar.

Kwamishinan 'yan sanda ya ce, hukumar ta samu nasarar cafke matashin, Umaru Shehu, da mallakar wasu kananan bindigu 11 da ya kudirci mika su ga 'yan baranda masu hana tsugunno da walwala a jihar.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar a halin yanzu na ci gaba da ribatu da wasu bayanai na Matashin domin bankado sauran miyagu makamantan sa ma su yaki da zaman lafiya da hana ruwa gudu na ci gaban al'umma.

Babban jami'in na 'yan sanda ya kuma ce, hukumar ta cikwikwiye kugun wasu ababen zargi 41 masu hannu cikin mummunar zanga-zangar da ta auku a karamar hukum Tsafe ta jihar a ranar 24 ga watan Dasumba na shekarar bara.

KARANTA KUMA: Lafiya Jari: Amfanin Kokwamba ga lafiyar Dan Adam

An kamu samu nasarar ceto wata Mata, Ayobami Dauda, da ta yi kacibus da azal wajen fadawa hannun masu garkuwa da mutane a kan hanyarta ta dawowa daga birnin Zazzau.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, Zannah wanda ya ci gajiyar kujerar tsohon kwamishinan 'yan sanda na jihar Zamfara, Mista Belel Usman, ya ce ana ci gaba da fuskantar barazana ta ta'addancin ma su garkuwa da mutane, satar shanu, rikicin makiyaya da manoma, kisan gilla da zubar da jinin al'umma ba tare da hakki ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel