PDP ta rasa mambobinta 450 a Akwa Ibom

PDP ta rasa mambobinta 450 a Akwa Ibom

- Jam’iyyar PDP ta rasa mambobinta sama da 450 a karamar hukumar Udung Uko da ke jihar Akwa Ibom inda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

- Masu sauya shekar sun koma APC ne a wani ziyara da suka kai ofishin kamfen din jam’iyyar da ke Uyo

- Jagoran tafiyar yace zuwansu APC daida yake da nasarar jam’iyyar a dukkanin zabe a Udung Uko

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Udung Uko da ke jihar Akwa Ibom ta rasa mambobinta sama da 450 inda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasar.

Masu sauya shekar sun koma APC ne a jiya Laraba, 9 ga watan Janairu lokacin wani ziyara da suka kai ofishin kamfen din jam’iyyar da ke Uyo.

Sun samu jagorancin Mista Obosio Obisio, shugaban matasan PDP a karamar hukumar Udung Uko, Messrs Peter Effanga da Sam Effiong, jami’an jam’iyyar reshen yankin da Ulap Nyong Edumoh, shugaban makaranta Dominic Comprehensive College, makaranta mafi shahara a yankin.

PDP ta rasa mambobinta 450 a Akwa Ibom

PDP ta rasa mambobinta 450 a Akwa Ibom
Source: Depositphotos

Mista Obiosio yace zuwansu APC daida yake da nasarar jam’iyyar a dukkanin zabe a Udung Uko, daya daga cikin kananan hukumomi biyar da ke yankin Oron, kabila mafi girma na uku a jihar Akwa Ibom

Ulap Edumoh ya bayyana cewa sun koma APC ne saboda gudunawar da Obong Nsma Ekere, dan takarar gwamna na jam’yyar ya bayar ga al’umman Oron tare da gina hanyoyi a matsayinsa na manajan darakta na kungiyar ci gaban Niger Delta.

KU KARANTA KUMA: Kingsley Mogahalu ya kashe fiye da Naira Miliyan 200 a kan takaran 2019

Dr Amadu Attai, mataimakin dan takarar gwamnan APC wanda ke wakilya Obong Ekere, yace an shirya sauya shekar ne kafin kamfen din APC a Udung Uko wanda za a gudanar yan makonni masu zuwa saboda masu sauya shekar sun ce ba za su iya jira ba.

Da yake tarban masu sauya shekar a madadin shugaban APC na ihar, Dr Ita Udosen, mataimakin shugaban APC a jihar, ya yaba masu da suka banbance haske fa duhu sannan suka dawo APC sannan yace masu za a basu dama daidai da na tsoffin yan jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Leit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel