Kingsley Mogahalu ya kashe fiye da Naira Miliyan 200 a kan takaran 2019

Kingsley Mogahalu ya kashe fiye da Naira Miliyan 200 a kan takaran 2019

Mun samu labari daga Jaridar The Cable cewa Kingsley Mogahalu wanda yana cikin masu harin kujerar shugaban kasa a zaben bana na 2019 ya kashe akalla Naira Miliyan 200 kawo yanzu wajen neman takara.

Kingsley Mogahalu ya kashe fiye da Naira Miliyan 200 a kan takaran 2019
Aljihun Moghalu yayi kuka a kan takarar kujerar shugaban kasa
Source: Instagram

Kingsley Moghalu, wanda ya fito takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta YPP yace ya batar da abin da ya haura Naira miliyan 200 daga aljihun sa. Moghalu ya bayyyana wannan ne lokacin da ya zauna da jama’a a wata hira da NTA jiya.

‘Dan takarar ya bayyana cewa bai da wani uban gida da ya tsaya masa, don haka da kudin sa yake amfani wajen neman takarar shugaban kasa, sannan kuma ya bayyana cewa zai samu sauran kudin kamfe ne daga masu bada gudumuwa.

KU KARANTA: Saraki ya cire kudi daga aljihun sa ya biya Mutanen Kwara albashi

Moghalu ya nuna cewa idan har yayi nasarar zama shugaban kasa a 2019, zai habaka tattalin arzikin Najeriya ta hanyar tallafawa kananan sana’o’i da. Moghalu yace a matsayin sa na mai ilmi, zai yi kokarin ganin ya gyara kasar nan.

Tsohon mataimakin gwamnan na babban bankin CBN, bako ne a harkar siyasa, sai dai yayi alkawarin cewa kudin da aka warewa tsare-tsaren da ke taba rayuwar talaka irin su N-Power za su isa ga wadanda ke bukata idan ya kafa gwamnati.

Gidan talabijin na NTA ne su ka shirya wannan shiri da taimakon hukumar nan ta Daria Media da kuma gidauniyar nan na MacArthur Foundation. ‘Dan takarar yayi magana na kusan sa’a 2 a gaban Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Online view pixel