Bukola Saraki ya cire kudin hannun sa ya biya Ma’aikata albashin Miliyan 16.9

Bukola Saraki ya cire kudin hannun sa ya biya Ma’aikata albashin Miliyan 16.9

Mun samu labari a makon nan cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Abubakar Bukola Saraki, ya biya wasu daga cikin ma’aikatan jihar Kwara bashin albashin da su ke bin gwamnati na tsawon lokaci.

Bukola Saraki ya cire kudin hannun sa ya biya Ma’aikata albashin Miliyan 16.9

Saraki ya biya Mutanen Kwara da ke bin Gwamnati bashi kudin su
Source: UGC

Bukola Saraki ya cire kudi har Naira miliyan 16.9 daga cikin aljihun sa ya biya ma’aikatan karamar hukumar Irepodun da ke cikin jihar Kwara kudin da su ke bi bashi. Shugaban wannan karamar hukumar ya bayyana hakan.

Muyiwa Oladipo wanda shi ne shugaban karamar hukumar Irepodun ya bayyana cewa wannan namijin kokari da tsohon gwamnan yayi, yana cikin yunkurin da yake yi wajen ganin ma’aikatan jihar Kwara sun samu sa’ida.

KU KARANTA: Gwamnatin Jihar Neja Ta Rufe Babban Gidan Shaye Shaye

Oladipo yace shugaban majalisar kasar ya cika alkawarin da ya dauka a bara na kawo dauki ga ma’aikatan yankin jihar da kudin su su ka makale bayan adadin kudin da jihar ta ke samu daga gwamnatin tarayya ya ragu.

Jagororin hukumar kwadago na kasa watau NLC ta yabawa wannan abin kwarai da shugaban majalisar dattawan na Najeriya yayi. Haka kuma ma’aikatan kananan hukumomin sun jinjinawa Bukola Saraki da wannan gagarumin agaji.

Shugaban karamar hukumar ta Irepodun da ke jihar Kwara yake cewa wannan taimako da Saraki yayi wa mutanen Garin Omu-Aran zai taimaka wajen rage radadin da wannan Bayin Allah su ke ciki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel