Da ikon Allah: Zamu kawo karshen kashe kashe a Birnin Gwari – El-Rufai

Da ikon Allah: Zamu kawo karshen kashe kashe a Birnin Gwari – El-Rufai

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na aiki tukuru ba dare ba rana wajen ganin ya kawo karshen ayyukan yan bindiga dake kai hare hare a yankin karamar hukumar Birnin Gwari.

Majiyar Legit.com ta ruwaito El-Rufai ya bayyana haka ne a yayin taron sauraron ra’ayin jama’a a yayin daya kai ziyarar yakin neman zabe a takarar da yasa a gaba na zarcewa akan kujerar gwamnan jahar Kaduna.

KU KARANTA: Siyasar Kano; Ganduje ya rantsar da sababbin kwamishinoni guda 4

Da ikon Allah: Zamu kawo karshen kashe kashe a Birnin Gwari – El-Rufai

El-Rufai
Source: Facebook

A jawabinsa, gwamnan ya tabbatar ma jama’an Birnin Gwari cewa hukumomin tsaron Najeriya sun samu bayanan sirri dake nuna sakamakon hare haren da dakarun Sojin Najeriya ke kaiwa a jihohin Zamfara da Katsina, yan bindiga sun fara dawowa garuruwan Birnin Gwari da Chikun na jahar Kaduna.

Da wannan ne shugaba Buhari ya bada umarnin kafa wata sabuwar sansanin Sojoji data Yansanda don kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin, tare da tabbatar da tsaro, wanda yace a yanzu haka an kammala gininsu duka.

Da ikon Allah: Zamu kawo karshen kashe kashe a Birnin Gwari – El-Rufai

Birnin Gwari
Source: Facebook

Bugu da kari El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta umarci kamfanin Aliko Dangote dasu sake gina babbar hanyar data hada garin Kaduna, Birnin Gwari har zuwa iyakan Birnin Gwari da jahar Neja, inda yace a yanzu haka Dangote ya ware naira biliyan 5 don gudanar da wannan aikin.

Daga karshe gwamnan ya danganta matsalar tsaron da aka samu a karamar hukumar Birnin Gwari da gazawar shugabanci a karamar hukuma da kuma nuna bambamci da wariya da rashin adalci da ake nunawa a shugabancin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel