Buhari ya amince da kashe naira biliyan 2.6 don gina hanyar Sharada zuwa Madobi

Buhari ya amince da kashe naira biliyan 2.6 don gina hanyar Sharada zuwa Madobi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da aikin sake ginin babbar hanyar data tashi daga unguwar Sharadan jahar Kano zuwa garin Madobi ta karamar hukumar Madobi, garin tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Ministan ayyuka, lantarki da gidaje, Babatunde Raji Fashola ne ya sanar da haka a ranar Laraba, 9 ga watan Janairu jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa daya gudana a fadar gwamnatin Najeriya.

KU KARANTA: Siyasar Kano; Ganduje ya rantsar da sababbin kwamishinoni guda 4

A jawabinsa, Fashola yace shugaba Buhari ya amince a kashe kudi naira biliyan biyu da miliyan dari bakwai (N2,600,000,000) wajen aikin sake gina babbar hanyar Sharada zuwa Madobi, haka nan ya amince a kashe naira biliyan ashirin da uku da miliyan dari takwas, N23.8bn, don sake gina hanyar New Bussa zuwa Kaiyaa da suka hada jihohin Kwara da Neja.

Bugu da kari Fashola yace gwamnatin Najeriya ta amince da kafa dokar kulawa da gine gine gwamnati, wanda zata samar da ayyukan yi gay an Najeriya, tare da tabbatar da adadin kadarori mallakin gwamnatim tarayya.

“Muna da kwararrun ma’aikata masu sana’ar hannu, amma ba’a tanadar musu da ingantaccen yanayin da zasu gudanar da aikinsu ba, akwai matasa masu aikin sanya tangaran tayil, leburori, masu hada famfunan ruwa, kafintoci da sauransu.

“Don haka zamu fara aiki da dokokin nan, ta yadda zasu taimaka wajen kula da duk wasu gine ginen gwamnati, wannan doka za ta bamu kidayan ire iren ayyuka ko gyare gyare da kowanni ginin gwamnati ke bukata, da kuma yadda za’a gudanar da aikin cikin sauki.” Inji shi.

Daga karshe Fashola yace gwamnati ta amince a kashe naira miliyan dari takwas da goma sha biyu da dubu dari biyar don aikin ware wasu yankuna na musamman da za’ayi amfani dasu wajen aikin ginin tashar wutar lantarki ta Mamabilla.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel