Takarar shugaban kasa ta raba kan mutanen Kudancin Najeriya

Takarar shugaban kasa ta raba kan mutanen Kudancin Najeriya

Mun fahimci cewa Manyan kasar Ibo da ake kudancin Najeriya sun shiga wani hali mai rudarwa a game da babban zaben da za ayi shekarar nan inda Atiku Abubakar zai kara da shugaba Muhammadu Buhari.

Takarar shugaban kasa ta raba kan mutanen Kudancin Najeriya

Ana samun sabanin ra'ayin tsakanin mutanen Kudancin Najeriya a kan zaben 2019
Source: UGC

Wasu daga cikin jagorin kasar Inyamurai sun shiga rudu a game da wanda za su marawa baya tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma ‘dan takarar PDP, Atiku Abubakar a 2019 kamar yadda jaridar Vanguard ta fada.

Shugaban kungiyar nan mai rajin kafa lasar Biyafara ta MASSOB watau Uchenna Madu, ya bayyana cewa ko shugaban kasa Buhari ya ci zabe, ko ma ya sha kasa a 2019, mutumin kasar Ibo ba zai samu shugabancin Najeriya ba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ba zai mikawa Bola Tinubu mulki ba inji Atiku

Madu ya caccaki sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda yake kira ga Ibo su marawa APC baya idan har su na so su karbi mulki bayan 2019. Shugaban kungiyar ta MASSOB yana ganin akwai tsabar yaudara a lamarin.

Shi kuma wani Sarkin kasar Ihim da ke yankinn Mbano a cikin jihar Imo, bai yi na’am da ra’yin kungiyar MASSOB ba, inda a cewar Mai martaba Oliver Ohanwe, idan har Ibo su na neman mulkin Najeriya, kurum su bi bayan APC.

Wani mai fada a ji a yankin kasar obo, Emeka Diwe, wanda shi ne shugaban wata kungiya ta “South-East Town Unions”, ya fadawa ‘yan jarida cewa mutanen Ibo za su samu mulki ne idan su ka shiga tafiyar Atiku Abubakar da Peter Obi.

KU KARANTA: Wani Gwamnan APC yana kokarin zaben Atiku a jihar sa - PDP

Emeka Diwe yana ganin bai kamata Inyamurai su tsaya su na dakon 2023, yayin da su ke damar daura mataimakin shugaban kasa a 2019 ba. Shi ma dai shugaban majalisar Inyamurai na kasa watau Chilos Godsent yana kan wannan ra’yi.

Shugaban kungiyar na INC, Chilos Godsent, ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta maida mutanen kudu maso gabas, saniyar ware. Don haka ne Dattijon yake ganin ya kamata jama’a su bi bayan Peter Obi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel