Babban Magana: Buhari ba shi da wata kima, yaki da rashawa karyace – Inji Bukola Saraki

Babban Magana: Buhari ba shi da wata kima, yaki da rashawa karyace – Inji Bukola Saraki

Tsohon gwamnan jahar Kwara, kuma shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ya bayyana cewa gwamnatin Buhari a cike take da barayi masu wawuran kudaden al’umma, don haka duk wani mutunci da Buhari ke da ita ya zube wanwar.

Legit.com ta ruwaito Saraki ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba 9 ga watan Janairu, inda yace sakamakon yadda Buhari ke lamuntar barayi marasa gaskiya na kusantarshi, hakan ya keta masa rigar mutunci.

KU KARANTA: Ban cire rai ba, zan cigaba da masa addu’ar shiriyar Allah – Inji Mahaifin wani dan Boko Haram

Baban Magana: Buhari ba shi da wata kima, yaki da rashawa karyace – Inji Bukola Saraki

Bukola Saraki
Source: UGC

“Ko shakka babu akwai barayi a gwamnatin nan, kuma idan har da gaske Buhari na yaki da rashawa, toh ya aka yi an kama wani jigo a gwamnatinsa da rashawa, amma har yanzu babu tuhuma dake kansa balle kuma a gurfanar da shi gaban kotu.

“A ganina idan har ka kasance irin haka, tabbas baka da sauran bakin da zaka ce mana wai kana yaki da rashawa kuma na yarda, bai kamata ace akwai wadanda suka fi karfin doka ba, dole ne ka nuna cewa doka zata hau kan duka wanda ya karyata.” Inji Saraki.

Bugu da kari, Saraki, wanda shine daraktan yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kara da cewa idan aka duba yadda Buhari ke daga ma na kusa da shi kafa, a iya cewa shi kansa ma barawo ne, saboda dole ne ka dauki laifin duk abinda ya faru a gwamnatinka.

Idan za’a tuna Legit.com ta ruwaito a watan Yulin shekarar 2018 ne Saraki ya fice daga jam’iyyar APC ya koma jam’iyyar PDP sakamakon takun saka irin ta siyasa tsakaninsa da jigogin APC musamman Bola Ahmed Tinubu, da kusoshin gwamnatin Buhari.

Daga karshe Saraki ya caccaki gwamnatin Buhari ta yadda ta kuntata ma yan Najeriya da hakan yayi sanadiyyar mutane miliyan 20 suka rasa ayyukansu, sa’annanya soki gwamnatin bisa cigaba da biyan kudin tallafin man fetir, wanda yace shima wani nau’I ne na rashawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel