EFCC ta roki Kotu a cigaba da shari’a ko da Dasuki ba ya hallarar zaman Kotu

EFCC ta roki Kotu a cigaba da shari’a ko da Dasuki ba ya hallarar zaman Kotu

A Ranar Laraba ne aka sake komawa gaban alkali a kotu domin cigaba da shari’ar da ake yi tsakanin gwamnatin Najeriya da kuma tsohon mai bada shawara kan harkar tsaro na kasar watau Sambo Dasuki.

EFCC ta roki Kotu a cigaba da shari’a ko da Dasuki ba ya hallarar zaman Kotu

Lauyan Hukumar EFCC ya nemi a cigaba da binciken Dasuki
Source: Getty Images

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Premium Times, an gaza cigaba da shari’ar da ake yi tsakanin Sambo Dasuki da sauran wadanda gwamnatin Buhari ta ke tuhuma a gaban wani abban kotun tarayya da ke zama a Abuja.

Alkali mai shari’a ya gagara cigaba da gudanar da bincike ne a dalilin rashin bayyanar wanda ake zargi. Tun 2015 aka damke Sambo Dasuki inda ake zargin sa da yin gaba da wasu makudan kudin da aka ware domin sayen makamai.

Sambo Dasuki wanda ya rike mukamin NSA a lokacin tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya sha alwashin cewa ba zai sake bayyana a gaban kotu ba har sai ranar da gwamnatin tarayya ta bi umarnin da aka ba ta na bada belin sa.

KU KARANTA: Saboda Buhari aka samu rangwamin ta'adin Boko Haram - Okorocha

Babban Lauyan gwamnati mai suna Oluwaleke Atolagbe, ya fada mana cewa an gaza cigaba da shari’ar a jiya tun da wanda ake zargi ya ki bayyana a gaban kuliya. Lauyan na EFCC ya nemi kotu ta cigaba da aiki ko da Dasuki bai zo ba.

Lauyan wanda ake tuhuma watau Victor Okudili ya nemi kotu ta dage wannan kara har sai illa ma sha Allahu a dalilin rashin bin umarnin kotu da hukumar EFCC ta yi. Yanzu dai Lauyan gwamnati zai duba wannan roko da Dasuki yake yi.

Ana binciken Dasuki ne tare da Bashir Yuguda, Sagir Attahiru da Attahiru Dalhatu Bafarawa, da kuma kamfanin Dalhatu investment Ltd. Dasuki ya rantse dai cewa ba zai sake hallara a gaban kotu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel