Jam'ian kwastam sun kama kwaya ta miliyoyi a Kaduna

Jam'ian kwastam sun kama kwaya ta miliyoyi a Kaduna

Hukumar kwastam shiyya ta 'B' dake Kaduna ta sanar da cewar ta kama kwalayen kwayar Tramol 225mg da bahunhunan shinkafar kasar waje 1,100 da darajar su ta wuce miliyan N54m.

Shugaban ofishin shiyyar, Mohammed Sarkin Kebbi, ne ya bayyana hakan a yau, Laraba, yayin gabatar da kayan da suka kama ga manema labarai.

Sarkin Kebbi ya bayyana cewar jami'an kwastam sun kama kwayoyin da Ka boye a wasu manyan motoci dake dauke da sassan babur din hawa a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Ya kara da cewar sun yi nasarar gano kwayoyin ne ta hanyar samun bayanan sirri daga wasu 'yan kasa nagari, tare da bayyana cewar darajar kwayar Tramol din ta wuce miliyan N15m a kasuwa.

Jam'ian kwastam sun kama kwaya ta miliyoyi a Kaduna

Jam'ian kwastam sun kama kwaya ta miliyoyi a Kaduna
Source: UGC

Kazalika ya bayyana cewar sun kama shinkafar kasar waje 1,100 a watan Disamba na shekarar 2019 zuwa farkon watan Janairu da muke ciki.

"Mun kama wasu motoci 10 na haramtattun kayan da aka shigo dasu. Wannan ba kankanuwar nasarar ba ce ga ofishin shiyyar 'B' na hukumar kwastam," a cewar Sarkin Kebbi.

DUBA WANNAN: Wole Soyinka ya fadi abinda zai iya haddasa yakin duniya na 3

Kazalika ya jaddada aniyar hukumar Kwastam na dakile kwararowar miyagun kwayoyi zuwa cikin Najeriya.

"A matsayin mu na hukumar gwamnatin tarayya, zamu cigaba da bayar da gudunmawa wajen dakile matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi dake barazanar lalata rayuwar matasan mu.

"Kwayar Tramadol na matukar wahala yanzu, hakan ya sa tana tsada yanzu a kasuwa," a cewar Sarkin Kebbi.

Kazalika ya yi kira ga jama'a da suke taimaka wa jami'an kwastam da bayanai domin samun nasarar cafke ragowar kwayar Tramol da aka shigo da ita cikin kasar nan musamman a yankin arewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel