Saboda Buhari aka samu rangwamin tsanani a Arewa maso Gabas - Okorocha

Saboda Buhari aka samu rangwamin tsanani a Arewa maso Gabas - Okorocha

- Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya ce shugaba Buhari ya taka rawar gani wajen kawo rangwamin tsanani na ta'addanci a Arewa maso Gabas

- Rochas ya bayyana damuwar sa kan yadda ake cin fuskar jagorori yayin rayuwar su kuma a yi ma su kyakkyawan bita-da-kulli bayan ajali ya katse ma su rabo

- Gwamnan ya ce tilas ne yabawa kwazo da bajintar shugaba Buhari a bisa karagar mulki

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya ce sakamakon kwazo da kuma bajintar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa kujerar jagoranci ya sanya aka samu rangwamin tsanani na ta'addanci a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Gwamna Rochas ya ce ko shakka ba bu shugaban kasa Buhari na ci gaba da taka muhimmiyar rawar gani wajen kawo karshen ta'addancin masu tayar da kayar da baya na Boko Haram a Arewa maso Gabashin kasar nan.

A sanadiyar wannan lamari da dukkanin bajintar shugaba Buhari da ta yi tasirin gaske wajen samun nasarori ya sanya gwamna Rochas ke kira ga daukacin al'ummar Najeriya wajen yiwa shugaban kasa kyakkyawan bita-da-kulli yayin rayuwa gabanin ajali ya cimma sa.

Saboda Buhari aka samu rangwamin tsanani a Arewa maso Gabas - Okorocha

Saboda Buhari aka samu rangwamin tsanani a Arewa maso Gabas - Okorocha
Source: UGC

Gwamnan ya yi wannan kira ne a yau Laraba cikin fadar gwamnatin sa da ke birnin Owerri, inda ya bayyana takaicin sa dangane da yadda ake cin fuskar jagorori yayin rayuwa kuma a yi ma su kyakkyawan bita-da-kulle bayan da ajali ya katse ma su hanzari.

Ya ci gaba da cewa, ya kamata al'ummar Najeriya su hankaltu wajen yabawa bajinta da kwazon jaruman kasar nan a yayin rayuwa da bayan mutuwar sa sakamakon kishi da kuma soyayya da ta sanya suka sadaukar da kawunan su wajen yiwa kasar su gagarumar hidima.

KARANTA KUMA: Jeff Bezos, mai kudin duniya zai tsinke igiyar aure da Matar sa

Sabanin adawa, gwamna Rochas ya ce tilas ne a yabawa bajinta da kwazon shugaban kasa Buhari da kishin kasa ya sanya ya ti tsayar daka ba bu dare ba bu rana wajen yakar ta'addanci masu muguwar ta'ada a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hudumar sojin kasa ta Najeriya ta samu nasarar cafke wasu muggan makamai na kare dangi a hannun masu mummunar ta'ada cikin karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel