Zaben 2019: Ba zan yadda a fiddo kudin gwamnati ayi zabe ba - Buhari

Zaben 2019: Ba zan yadda a fiddo kudin gwamnati ayi zabe ba - Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada alkawarin da ya dauka a kwanakin baya na cewa ba zai yadda a fiddo koda kwabo ba daga baitul-malin tarayya domin yin siyasa da su ba.

Shugaban kasar ya bayar da wannan tabbacin ne dai a cikin wani sako da ya wallafa a shafin sa na dandalin sada zumunta na Tuwita.

Zaben 2019: Ba zan yadda a fiddo kudin gwamnati ayi zabe ba - Buhari

Zaben 2019: Ba zan yadda a fiddo kudin gwamnati ayi zabe ba - Buhari
Source: Twitter

KU KARANTA: An fatattaki karuwai a wata jihar Arewa

Legit.ng Hausa haka zalika ta samu cewa shugaba Buharin ya kara da cewa shi ya yadda ko dai zai fadi ba zai yadda kowa ya dauki sisi ba yayi yakin neman zaben shi ba ko ma na wani can.

Ya kara da cewa ko da kuwa wannan ne kadai canjin da zai kawo a kasar, to tabbas ya shirya sai ya tabbatar da hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel