Jihar Filato dai ta Buhari ce, inji Lalong

Jihar Filato dai ta Buhari ce, inji Lalong

- Kungiyar dattawan APC na jihar Filato tace nasarar shugaba Buhari da Lalong tabbas ne

- Shugaba Buhari bashi da abokin takara a zabe mai zuwa

- 'Takara daban, nasara daban'

Jihar Filato dai ta Buhari ce, inji Lalong

Jihar Filato dai ta Buhari ce, inji Lalong
Source: UGC

Kungiyar dattawan jam'iyyar APC a jihar Filato tace nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Simon Lalong a zabe mai zuwa tabbas ce.

Ofishin dillancin labarai na NAN, ya ruwaito cewa Buhari da Lalong duk yan jam'iyyar APC na neman komawa kujerun su ne a zaben da za'ayi a 16 ga watan Fabrairu da 2 ga watan Maris.

Jethro Akun, shugaban kungiyar dattawan, reshen tsakiyar jihar Filato ya fadi hakan a ranar laraba a garin Jos yayin bude taron da kungiyar tayi.

Mista Akun, tsohon mataimakin gwamnan jihar Filato yace abinda suka gani a taron bude yakin neman zaben APC da akayi a 4 ga watan Janairu ya nuna cewa akwai nasara nan gaba.

GA WANNAN: Hukumci: An kulle matsashin da ya tsiyayar wa da makwabcinsa ido

"Wasu daga cikin mu, zamu iya cewa shugaban kasa bashi da abokin adawa a zabe mai zuwa. Eh, akwai wadanda ke takarar kujerar da yake nema, wannan itace damokaradiyya, amma babu wanda ya dace da takara dashi. A matakin jiha kuwa, mutanen da muka gani masu goyon bayan mu suna da yawa. Da abinda muka gani gaskiya an gama zabe. Mun san akwai yan takara amma takara daban da cin zabe," inji shi.

Yace taron dattawan anyi shi ne don hadin kan samun nasara a duk zabuka masu zuwa.

A jawabin Joseph Din, shugaban kungiyar dattawan APC na jihar Filato, ya roki mutane da su cigaba da hakuri da jam'iyyar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel