Gwamna Fayemi na tadiye kokarin zabar Atiku a jihar Ekiti - PDP ta koka

Gwamna Fayemi na tadiye kokarin zabar Atiku a jihar Ekiti - PDP ta koka

- Jam'iyyar PDP na zargin gwamnan jihar Ekiti da yunkurin hana su yakin neman zaben shugabancin kasa a jihar

- Hakan ya biyo bayan rashin amincewa da amfani da filin wasan dake babban birnin jihar

- Gwamnan ya musa hakan cewa da ana gyaran filin wasan ne

Gwamna Fayemi na tadiye kokarin zabar Atiku a jihar Ekiti - PDP ta koka

Gwamna Fayemi na tadiye kokarin zabar Atiku a jihar Ekiti - PDP ta koka
Source: Depositphotos

Jam'iyyar PDP reshen jihar Ekiti na zargin jam'iyyar APC karkashin jagorancin gwamnatin Kayode Fayemi akan yunkurin yanda zasu bata dan takarar shugabancin kasa Atiku Abubakar ta hanyar hana jam'iyyar gurin da zasu yi zagaye a ranar 14 ga watan Janairu don shirin zaben 16 ga watan Fabrairu mai zuwa.

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Ekiti, Gboyega Oguntuase, a yayin da ya zanta da manema labarai a ranar laraba a Ado Ekiti, yace Mista Fayemi yaki sakin Stadium din Oluyemi Kayode dake Ado Ekiti kuma da niyyar bata yakin neman zaben PDP.

Mista Oguntuase yace hakan ya kara tabbatar ma da jam'iyyar adawar cewa APC ta kosa tayi magudi tare da danne zaben 2019.

A maida martanin gwamnati a ranar 8 ga watan Janairu, 2019, wanda daraktan gudanarwa na kungiyar wasanni, a madadin manajan, Akinola P.A yace ana gyaran stadium din ne kuma an hana ababen hawa yawo a lokacin.

"An umarce ni da inyi magana akan wasikar ka ta ranar 2 ga watan Janairu, da ake bukatar yin kamfen da ita. Amma, akwai bukatar ku sani cewa ana gyara filin wasan don shirye shiryen wasan kwallon kafa na gaba. Akwai bukatar hana ababen hawa yawo a gurin na wannan dalili. Don haka ne muka hana amfani da gurin."

GA WANNAN: Za'a shiga yajin aiki ba tare da an sake baiwa gwamnati kashedi ba - Kwadago

Amma Fayemi ya kwatanta zargin da zance mai batarwa cewa da ma'aikatan gwamnati na maida amsar wasika ne dogaro da abinda ke faruwa kuma bashi da ta cewa akan maganar a matsayin shi na gwamnan jihar.

Mista Fayemi, wanda ya maida martani ta bakin babban mataimakin shi na musamman akan harkokin sadarwa, Segun Dipe yace: A lokacin da muka fara mulki kusan duk abubuwan nan basa halin da ya dace.

Har da kuma filin wasan a ciki. A matsayin gwamnatin da ta san abinda takeyi, dole ne mu dau matakin gyara. Kuma Fayemi ba zai taka hakkin wani ba. Ko PDP din ba ta hannun gwamnan ta nemi filin wasan ba amma kuma ta dawo tana dora mishi laifi," inji shi.

Shugaban PDP yace bai kamata ba da gwamnatin tayi shiru taki bada amsar wasikar su ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel