Yaudara ce kawai Buhari ya shirya wa ma'aikata kan N30,000 har ya zarce Fayose

Yaudara ce kawai Buhari ya shirya wa ma'aikata kan N30,000 har ya zarce Fayose

- Shugaban kasa Muhammad Buhari yana wasa da hankalin ma'aikata akan karin albashi.cewar Fayose

- Ya kamata ma'aikata su farga da manufar sa na kafa sabon kwamiti

- Yayi hakan ne dan su bashi kuri'un su a zabe mai zuwa duba da furucin da sukayi na ba zasuyi zabe ba matukar ba'a kara musu albashi ba

Yaudara ce kawai Buhari ya shirya wa ma'aikata kan N30,000 har ya zarce Fayose

Yaudara ce kawai Buhari ya shirya wa ma'aikata kan N30,000 har ya zarce Fayose
Source: Depositphotos

Duba da sabon kwamiti da shugaban kasa Muhammad Buhari ya kafa dangane da maganar karin albashi, tsohon gwamnan jihar Ekiti Mr Adeyole Fayose yace wannan duk wani shiri ne na kokarin cimma manufar sa.

Yace shugaban kasar ya jijjiga da jin hukuncin da kungiyar kwadago NLC ta yanke na cewar ba zasuyi zabe ba matukar ba'ayi musu karin albashi ba.

Dangane da batun da aka fitar a ranar Laraba na kafa sabon kwamiti Fayose yace menene amfanin kwamitin tunda ya amince da maganar kuma zai mikata zuwa majalisa tun watanni Uku da suka gabata.

GA WANNAN: Don Allah kada ku bar makiyaya suyi kiwo a jiharmu - Ortom ga Sarakunansa

"Shugaban kasar yana wasa da hankalin ma'aikata ne kawai dan ya samu su kada masa kuri'a"

Ya kamata ma'aikata su farga su fahimci cewa shugaban kasar yana da wani buri ne shiyasa ya bullo da wannan hanyar.

Ya kara jaddada cewa shugaban kasar bazai iya bawa yan Najeriya mafita ba akan matsalolin su .

Sannan babu wani kwamiti da zai tankwasa ma'aikata su kara zabar gwamnatin da bata cancanta ba dan kara tafiyar da kasar tsayin wasu shekaru hudun.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel