Yadda wani labarin bogi ya kusa haddasa wa aure na matsala - Osinbajo

Yadda wani labarin bogi ya kusa haddasa wa aure na matsala - Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana yadda labarin bogi ya kusa haddasa masa matsala da matar sa, Dolapo Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasar ya ce wata kafa ta yada labarin karya dake nuna cewar an kama shi da wasu mata dake rawa tsirara

- A cewar Osinbajo, kafar yada labaran ta saka kanun labarin da gangan bayan ya gana da wasu mata dake sanye cikin suturar su ta mutunci

Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasa, ya koka a kan illolin dake tattare da yada labaran bogi, yana mai bayyana yadda wani labarin bogi ya kusa haddasa masa matsala da matar sa, Dolapo Osinbajo.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne yau a wurin wani taron jaridar BBC a kan illolin dake tattare da kirkira da yada labaran bogi.

Osinbajo ya ce an saka wani hotonsa da wasu mata dake rawa tsirara bayan hakan bata faru ba.

Yadda wani labarin bogi ya kusa haddasa wa aure na matsala - Osinbajo

Osinbajo da Dolapo
Source: Depositphotos

Ya kara da cewar tabbas ya dauki hoto da wasu tawagar mata amma ba cikin shigar da aka nuna a labarin da ya gani ba.

A cewar sa, kafar yada labaran data wallafa labarin ta dauki hoton matan cikin wata shiga daban tare da yin amfani da shi wajen nuna cewar ya gana su a hakan.

DUBA WANNAN: Zabe: Alkalin alkalai na kasa ya aika sako na musamman ga dukkan alkalan

"Nima naga illar yada labaran bogi. Irin wadannan labarai na bogi kan iya kashewa mutum aure. Sati uku da suka wuce matata ta kira ni tare da tambaya ta abinda ya hada ni da mata dake rawa tsirara, sai na tambaye ta "me kike nufi da wannan tambaya?", sai ta fada min cewar ta karanta labari a wata jarida cewar an kama ni da wasu mata dake rawa tsirara.

"Bayan mun gama magana sai na duba tlabarin, sai ga hotona an hada shi da matan da na gana da su amma kuma cikin wata shigar daban ba wacce muka yi hoto da su ba.

"Da na duba sosai sai naga tabbas matan ne amma cikin shigar su ta rawa tsirara ba irin shigar da muka dauki hoto tare ba," a cewar Osinbajo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel