Da dumin sa: Buhari ya amince da gida sabbin jami'o'i 4 a fadin Najeriya

Da dumin sa: Buhari ya amince da gida sabbin jami'o'i 4 a fadin Najeriya

Majalisar zartaswa ta tarayyar Najeriya da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake shugabanta a zaman ta na yau ta amince da bayar da lasisi ga jami'o'i masu zaman kan su har guda hudu a fadin kasar.

Wannan dai na kunshe ne a cikin jawabin da Ministan ilimi, Adamu Adamu yayi wa 'yan jaridar fadar shugaban kasa, jim kadan bayan kammala zaman majalisar a garin Abuja babban birnin tarayya.

Da dumin sa: Buhari ya amince da gida sabbin jami'o'i 4 a fadin Najeriya

Da dumin sa: Buhari ya amince da gida sabbin jami'o'i 4 a fadin Najeriya
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wuraren da ba za muyi anfani da na'urar 'Card reader' ba a 2019 - INEC

Legit.ng Hausa ta samu cewa jami'o'in da aka amince da kafa su sune jami'ar Greenfield a Kaduna, jami'ar Dominion a garin Ibadan, jihar Oyo, jami'ar Trinity, jihar Ogun da kuma jami'ar Westland a garin Iwo, jihar Osun.

Ministan na ilimi ya kara da cewa an cimma matsayar ta amincewa da jami'o'in bayan an bincika an ga dukkan su sun cika sharuddan da gwamnatin ta gindaya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel