'Yan daba sun kai farmaki ofishin kamfen din Atiku a kudancin Najeriya

'Yan daba sun kai farmaki ofishin kamfen din Atiku a kudancin Najeriya

Kungiyar yakin neman zaben Atiku reshen jihar Ondo ta sanar da cewa wasu 'yan daban sun kai farmaki cikin dare a ofishinsu da ke Akure babban birnin jihar.

Jagoran kungiyar kuma dan takarar gwamna na PDP a jihar, Eyitayo Jegede ya ce a 'yan daba sun yiwa mai gadin ofishin duka ta yadda baya iya motsa jikinsa.

Mai magana da yawun kungiyar, Kayode Fasua ya ce wasu daga cikin 'yan daban da suka kai harin a ofishin yakin neman zaben Atikun da ke Ijapo a Akure suna yiwa jam'iyyar APC aiki ne.

'Yan daba sun kai farmaki ofishin kamfen din Atiku a kudancin Najeriya

'Yan daba sun kai farmaki ofishin kamfen din Atiku a kudancin Najeriya
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Da duminsa: 'Yan bindiga sunyi ta'addi a harin da suka kai kauyen 'Yar Santa a Katsina

"Sun kai farmakin a lokacin da jami'an tsaron da ke gadi a Ijapo sun tafi gida sannan suka farwa ofishin kamfen din mu," inji Fasua.

"Sun kai su 10 kuma sune dauke da bindigu. Sun yiwa mai gadinmu duka suka daure shi da igiya. Daga nan sai suka lalata allunan kamfen din Atiku da fostocinsa.

"Bayan haka sun lalata tagogin ofishin kuma suka rika tambaya a basu takardun mu. Da suka ka bukatarsu bata biya ba sai suka fara harbe-harbe.

"Wannan shine harin kwana-kwanan nan da wadanda ke rike da mulki keyi ta hanyar kai haro ofishin kamfen din abokan hamayya."

Mr Fasua ya yi kira ga jami'an tsaro su gudanar da bincike su binciko wadanda suka kai harin kuma a hukunta su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel