'Yan sanda sun tarwatsa taron 'ya'yan jam'iyyar PDP a jihar Jigawa

'Yan sanda sun tarwatsa taron 'ya'yan jam'iyyar PDP a jihar Jigawa

Wani labari da muka samu daga majiyoyin mu shine na yadda jami'an 'yan sandan Najeriya suka hana 'ya'yan jam'iyyar adawa ta PDP yin taro a garin Gumel dake jihar Jigawa ta Arewa maso yammacin Najeriya.

Wasu daga cikin wadanda abin ya faru akan idon su sun shaidawa majiyar ta mu cewa 'yan sandan sun hana taron ne bisa zargin shigowa da makamai da mahalarta taron suka yi yunkurin yi domin tayar da fitina.

'Yan sanda sun tarwatsa taron 'ya'yan jam'iyyar PDP a jihar Jigawa

'Yan sanda sun tarwatsa taron 'ya'yan jam'iyyar PDP a jihar Jigawa
Source: UGC

KU KARANTA: Ba zan iya biyan Naira dubu 30 mafi karancin albashi ba - Gwamna Ortom

Legit.ng Hausa haka zalika ta samu cewa 'yan sandan sun kuma zargi 'ya'yan jam'iyyar da kone kayan gwamnati da kuma kin sanar da hukumar 'yan sanda cewa za suyi taron.

'Yansandan dai sun tarwatsa taron ta hanyar yin amfani da barkonon tsohuwa, kana jami'an 'yan sandan sun toshe duk wasu hanyoyin shiga cikin garin Gumel domin tabbatar da doka da oda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel